Afirka

Sojojin ‘Yan Tawayen Habasha Sun Bar Babban Birnin Yankin Tigray.

Sojojin ‘yan tawaye a yankin Tigray na arewacin kasar Habasha sun janye na wucin-gadi daga babban birnin yankin, Mekelle, yayin da fadan da suke yi da sojojin gwamnatin tarayya ke matsowa kusa da birnin.

Kungiyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF), wacce ke tafiyar da harkokin yankin, ta bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne saboda fargabar hadarin da zai iya shafar fararen hula.

Wasu mazauna birnin Mekelle biyu sun ce yanzu sojojin da ke goyon bayan gwamnati ne ke iko da birnin, bayan da mayakan TPLF suka fice daga cikinsa. Wani daga cikin mazauna yankin ya kuma ce da alama an dawo da sabis na sadarwar wayar hannu a wasu sassan birnin.

KARANTA KUMA: Kungiyar AU ta yi kira da a kwantar da hankali yayin takaddamar da ke tsakanin Habasha, Masar da Eritrea

A ‘yan makonnin nan ne aka samu barkewar fada tsakanin TPLF da kawayenta a daya bangaren, da kuma sojojin gwamnati a wasu sassan yankunan arewacin kasar, wato Tigray, Afar da Amhara.

Wannan sabon yanayi ya nuna babban sauyi a rikicin, kuma yana haifar da fargaba ga masu sharhi cewa fadan na iya kara dagula al’amura a yankin Kahon Afirka, har ma ya jawo kasashen makwabta cikin rikicin.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yi kira ga dukkan bangarorin da su nuna “hakuri” da kuma “tattaunawa,” gabanin wani taron diflomasiyya kan rikicin da za a gudanar a kasar Masar a ranar Lahadi da ta gabata tare da shugabannin wasu kasashen makwabtan Habasha.

Shugabannin kasashen Masar, Eritrea, Somaliya da Sudan—wadanda dukkaninsu ke da dangantaka ta rashin jituwa da Habasha—sun gana a ranar Lahadi din da ta gabata a birnin El-Alamein na gabar tekun Masar.

Sun yi kira da a “girmama ikon mallakar kasa, hadin kai da kuma iyakokin kasashe,” tare da warware takaddama ta hanyoyin “lumana.”

Habasha na zargin kasashen Masar, Eritrea da Sudan da goyon bayan ‘yan tawayen Tigray, zargin da kasashen suka musanta.

Mazauna yankin Tigray na kokarin farfadowa daga mummunan yakin basasa na tsawon shekaru biyu wanda ya kare a shekarar 2022  bayan da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta shiga tsakani aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya da aka fi sani da Yarjejeniyar Pretoria tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai a cikin watanni shida da suka gabata an samu tabarbarewar dangantaka inda bangarorin biyu ke zargin juna da karya yarjejeniyar.

A watan da ya gabata kungiyar TPLF ta hada kai da wasu kungiyoyin dauke da makamai guda shida—ciki har da kungiyar ‘yan banga ta Fano daga yankin Amhara—domin kafa kawance mai manufar kawar da gwamnatin Firayim Ministan Habasha, Abiy Ahmed, daga karagar mulki. Wannan yakin basasa na daya daga cikin rikice-rikice mafi muni da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa a wannan karnin; inda wakilin sulhu na kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ya yi hasashen cewa kimanin mutane 600,000 ne suka rasa rayukansu yayin da rikicin ya jefa yankin cikin barazanar fuskantar matsananciyar yunwa.

A ranar Juma’a kasashen da ke makwabtaka da juna wato Habasha da Eritrea sun yanke alakar diflomasiyya tsakaninsu bayan da Addis Ababa ta zargi Asmara da goyon bayan wata sabuwar kawancen ‘yan tawaye – zargin da ita kuma Eritrea ta musanta.

Habasha ta kuma zargi Masar da goyon bayan ‘yan tawaye, wanda ya kai ga korar wani jami’in diflomasiyyar Masar, wanda Alkahira ta mayar da martani ta hanyar ba da umarnin wani jami’in ofishin jakadancin Habasha da ya bar ƙasar a cikin wannan lokacin.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa tabarbarewar yanayin tsaro a arewacin Habasha yana kawo cikas ga ayyukan jin kai kuma ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da su tabbatar da samun damar shiga ga mutanen da ke cikin mawuyacin hali cikin aminci da kuma ba tare da wata matsala ba.

Ethiopia da Masar sun shiga cikin takaddama mai tsawo kan Babbar Madatsar Ruwan Renaissance ta Habasha da aka gina a kan Kogin Nilu, wanda Alkahira ke fargabar zai iya rage rabon ruwan da take samu daga kogin.

A ranar Lahadi da ta gabata shugabannin huɗu da suka yi taro a Masar sun tabbatar da girmama ‘yancin kai da rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na ƙasashen yankin, yayin da suka yi kira da a bi dokokin ƙasa da ƙasa kan amfani da ruwan Nilu.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa, sun yi watsi da “matakan haɗin gwiwa” waɗanda za su iya cutar da ƙasashen da ke ƙasa, a wani ɓangare na nuni da tashin hankali kan madatsar ruwan Habasha.

 

 

BBC/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button