Najeriya

NUJ Reshen Jihar Nasarawa Ta Taya Celestina Cyril Murnar Lashe Zaben NAWOJ

Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Nasarawa ta taya daya daga cikin mambobinta Mrs. Celestina Cyril murnar zama Sakatariyar Shiyya ta D (Zone D) a karkashin kungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya (NAWOJ).

Mrs. Cyril wacce ke rike da mukamin Darakta a Hukumar Watsa Labarai ta Jihar Nasarawa (NBS) da ke Lafia ta samu wannan mukami na shiyya ne a yayin taron wakilan NAWOJ da aka kammala kwanan nan a birnin Kano a ranar Talata.

A cikin wata sanarwa a hukumance dauke da sa hannun Sakataren kungiyar na jihar Comrade Ibrahim Dauda reshen jihar Nasarawa ya bayyana matukar alfahari da nasarar da Cyril ta samu.Kungiyar ta nuna kwarin gwiwar cewa irin gudunmawar da ta bayar a baya a cikin kungiyoyin NUJ da NAWOJ za ta taimaka mata wajen gudanar da jagoranci mai inganci a matakin shiyya.

Da yake waiwayar lokacin da ta rike mukamin Shugabar NAWOJ a Jihar Nasarawa kungiyar ta yabi salon jagorancinta inda ta lura cewa ta sanya walwalar mata ‘yan jarida a gaba tare da tsayawa tsayin daka wajen kare mambobi daga barazana ko cin zarafi.

Sanarwar ta kuma yabi kwarewarta wajen karfafa hadin kai a cikin kungiyar tare da gina kyakkyawar alaka ta aiki da gwamnatin jiha kungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) da sauran kungiyoyi masu alaka da su domin ci gaban aikin jarida da kuma jihar baki daya.

Reshen NUJ na Jihar Nasarawa ya yi mata addu’ar samun hikima ilimi hangen nesa da kariyar Allah tare da bayyana kwarin gwiwar cewa za ta yi fiye da yadda ake tsammani a sabon mukaminta.

A karshe kungiyar ta taya Mrs. Cyril da dukkan al’ummar ‘yan jarida na Jihar Nasarawa murnar wannan gagarumar nasara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button