Najeriya

Katsina: Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 24 Sun Ceto Wadanda Aka Sace

Safina Umar Farouk

Jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga akalla 24 tare da dakile yunkurin sace mutane da yawa a kauyen Gidan Bawa a yankin Kandarawa na Karamar Hukumar Bakori a Jihar Katsina.

Wannan aiki ya samu hadin gwiwar sojojin Najeriya jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ‘yan kungiyar tsaro ta Katsina Community Watch Corps da kuma kungiyar Civilian Joint Task Force (CJTF).

Hukumar DSS ta bayyana cewa an gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri cewa wasu ‘yan bindiga masu dauke da makamai kimanin 40 wadanda ke biyayya ga wani babban dan bindiga mai suna Isiya Kwashen Garwa sun shirya kai hari a yankin tare da sace mazauna wurin musamman mata da yara.

 

KARANTA KUMA: ‘Yan sanda na kara karfafa tsaron al’umma da yaki da manyan laifuka masu haddasa tashin hankali

 

Wannan bayani ya sa jami’an DSS suka tattara ‘yan kungiyar Katsina Community Watch Corps da CJTF daga sansanin Guga domin tare maharan.

An ruwaito cewa tawagar tsaron ta yi wa ‘yan bindigar kwanton-bauna inda suka kashe 24 daga cikinsu tare da ceto mazauna kauyen da aka riga aka sace.

Haka kuma aikin ya kai ga kwato shanu 19 da aka sace daga al’ummar yankin.

DSS ta ce ‘yan bindigar sun shirya yin garkuwa da mutane da yawa irin wanda aka yi a al’ummar Woro a Jihar Kwara.

Ta ce an yi niyyar gudanar da wannan shirin ne domin kunyata gwamnati.

Jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyuka domin kamo sauran ‘yan kungiyar wadanda suka tsere daga wurin.

 

Safina Umar Farouk.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button