INEC Ta Sanya Sunan Adamu A Matsayin Dan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar SDP A Jihar Nasarawa.

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanya sunan tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Abubakar Adamu, a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Nasarawa.
Kungiyar yakin neman zaben Adamu ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na zamani da sadarwa na kungiyar Otaru Douglas, ya sanya wa hannu a Lafia babban birnin jihar.
Kungiyar ta bayyana sanya sunan a matsayin tabbacin takarar Adamu, inda ta ce hakan ya kawo karshen rade-radi da ce-ce-ku-ce game da wanda zai wakilci jam’iyyar a zaben gwamna mai zuwa.
KARANTA KUMA: APC ta lashe zaben cike gurbi na Sanatan Nasarawa ta Arewa
Ta ce wannan ci gaba ba zai hana kungiyar ci gaba da tuntubar masu kada kuri’a a kan shirye-shiryen da ta tsara ba a kananan hukumomi 13 na jihar.
A cewar sanarwar, muhimman abubuwan da kungiyar ta sa a gaba sun hada da inganta tsaro samar da ayyukan yi karfafa gwiwar matasa da mata da kuma inganta shugabanci mai mayar da hankali kan bukatun al’umma.
Kungiyar ta taya Adamu shugabancin jam’iyyar SDP na kasa da na jiha da kuma magoya bayan jam’iyyar murna kan wannan ci gaba tare da yaba wa jajircewarsu wajen yakin neman zaben.
Haka kuma ta yi kira ga mazauna jihar da sauran magoya baya da su shiga wannan tafiya, inda ta bayyana kwarin gwiwarta kan shirye-shiryen da jam’iyyar ta yi domin zaben mai zuwa.
Sai dai sanarwar ba ta bayar da karin bayani game da sanarwar ta INEC ko kuma takamaiman tsarin da hukumar ta bi wajen sanya sunan Adamu a matsayin dan takarar jam’iyyar ba.
Aisha.Yahaya, Lagos



