Kasashen Masar Da Eritrea Da Somaliya Da Sudan Sun Amince Da Hanyar Warware Rikici Cikin Lumina.

Kasashen Masar, Eritrea, Somaliya da Sudan sun yi kira da a samar da mafita ta siyasa da kuma ta hanyar zaman lafiya yayin da rikice-rikice ke karuwa a yankin, ciki har da yakin basasar Sudan da kuma manyan fada a Habasha.
Shugabannin kasashen hudu – Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi, Shugaban Eritrea Isaias Afwerki, Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud da kuma shugaban rundunar sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan – sun fitar da sanarwa ta hadin gwiwa a ranar Lahadi da ta gabata bayan wani taro da suka gudanar a birnin New Alamein na kasar Masar.
Habasha ta zargi Masar, Eritrea da Sudan da goyon bayan kawancen kungiyoyin masu dauke da makamai da ke yaki da gwamnatinta. Sai dai jami’ai daga dukkan kasashen ukun sun musanta hannu a cikin lamarin.
KARANTA KUMA: Sojojin ‘Yan Tawayen Habasha Sun Koma Daga Babban Birnin Yankin Tigray
Da farko a ranar Lahadi, el-Sisi ya bayyana cewa kalubalen da suka shafi kasashe makwabta suna bukatar “tattaunawa, ba gwabzawa ba.” Sanarwar ta nuna goyon baya ga gwamnatin sojin Sudan tare da yin kira da a bi hanyar siyasa karkashin jagorancin bangarorin siyasar Sudan.
Sudan na cikin yaki tun watan Afrilun 2023 tsakanin rundunar soji da kuma rundunar soji mai zaman kanta ta Rapid Support Forces (RSF). Sudan da Habasha sun yi musayar zarge-zarge game da tsoma baki a yakin basasar Sudan.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ya kamata kasashen da ke gabar teku su ci gaba da kula da Tekun Jan (Red Sea), matakin da ya zo a matsayin martani ga yunkurin Habasha – kasa mai iyaka da kasa kawai ba tare da hanyar shiga teku ba – na neman samun damar shiga teku da kuma kafa rundunar sojin ruwa.
Shugaban Somaliya Mohamud ya bayyana a ranar Asabar da ta gabata cewa Mogadishu ba ta da matsala idan Habasha ta samu damar gudanar da harkokin kasuwanci ta tashoshin jiragen ruwan Somaliya, muddin an cimma yarjejeniya da Somaliya kan hakan.
Masar da Sudan, wadanda suka dade suna takaddama da Habasha kan madatsar ruwa ta Grand Ethiopian Renaissance Dam da ke kan kogin Nilu, sun yi gargadi game da abin da suka kira “matakan da aka dauka ba tare da tuntubar sauran bangarori ba” wadanda ke cutar da kasashen da ke kasa a inda kogin ke bi.
An fitar da sanarwar ta hadin gwiwa ne a daidai lokacin da fada ke karuwa a Habasha tsakanin sojojin gwamnatin tarayya da kawancen kungiyoyi masu dauke da makamai guda bakwai, ciki har da kungiyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF), wacce ta yi yakin shekaru biyu mai tsanani da gwamnati, yakin da ya kare da yarjejeniyar zaman lafiya mai rauni a shekarar 2022.
Al Jazeera/Aisha.Yahaya, Lagos



