
An gurfanar da shugaban ‘yan adawar Zambia Brian Mundubile da tuhumar cin amanar kasa kuma yana ci gaba da zama a hannun ‘yan sanda tare da abokin takararsa a yayin da ake fama da tsananin tashin-tashinar siyasa a kasar.
An kama Mundubile ne a ranar Alhamis, bayan wani samame mai cike da tashin hankali da hukumomi suka kai wanda ya tilasta wa dan siyasar adawar boyewa.
Ya nuna rashin amincewarsa da sakamakon zaben shugaban kasa na baya-bayan nan a kasar wanda ya bai wa shugaba mai ci Hakainde Hichilema damar lashe wa’adi na biyu.
KARANTA KUMA: An Rufe Kotunan Zambia a Ranar Karshe ta Kalubalantar Sakamakon Zabe
Daga nan ne hukumomi suka zargi jam’iyyar Mundubile ta NRPUP da shirin tayar da kayar baya ta hanyar amfani da makamai zargin da jam’iyyar ta musanta.
A daren Asabar lauyan Mundubile Milner Katolo ya sanar da cewa an tuhumi wanda yake karewa da laifin cin amanar kasa.
Katolo ya shaida wa kafofin yada labarai na cikin gida cewa shugaban ‘yan adawar yana fatan amsa wannan tuhuma a gaban kotu.
Lauyan ya ce an kuma tuhumi wasu mutane 17 da laifin cin amanar kasa ciki har da abokin takarar Mundubile Makebi Zulu.
A cewar sakamakon hukuma Mundubile ya samu kashi 38 cikin 100 na kuri’u a zaben da aka gudanar a ranar 13 ga watan Agusta yayin da Hichilema ya samu kashi 60 cikin 100.
Washegarin zaben jami’an tsaro sun kai samame a wani gida da ke da alaka da Mundubile a babban birnin kasar Lusaka inda suka kashe wani tsohon minista tare da kama wasu ‘yan siyasa da dama.
Bayan samamen Mundubile da Zulu sun nemi mafaka a wani ginin Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin. An tsare su ne bayan shugaban kasar ya matsa wa Majalisar Dinkin Duniya lamba kan ta mika su ga hukumomi.
Jam’iyyar adawar ba ta samu damar kalubalantar sakamakon zaben a kotu ba kasancewar hukumomi sun rufe kotunan a ranar Litinin wadda ita ce ranar karshe ta shigar da kara.
Ana sa ran za a rantsar da Hichilema domin fara wa’adinsa na biyu a ranar 1 ga watan Satumba.
Masu sa ido na yankin da na kasa da kasa sun bayyana ranar zaben a matsayin mai cike da zaman lafiya amma Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Zambia ta yi kira da a dauki matakin gaskiya da bayyana halin da mutanen da ba a san inda suke ba bayan kama su da kuma ayyukan tsaro a lokacin zaben suke ciki.
BBC/Safina Umar Farouk.



