Fararen Hula Na Ci Gaba Da Kasancewa Yayin Da Sojojin Rasha Ke Ci Gaba Da Kai Hari A Ukraine
Garin Druzhkivka na Ukraine na fuskantar mummunan tasirin yakin yayin da sojojin Rasha ke ci gaba da matsowa kusa har sun kai nisan kilomita 15 lamarin da ya bar garin da motoci da suka kone, gine-gine da suka lalace da kuma tituna marasa mutane.
Mutane kalilan ne kawai suka rage a garin tare da sojojin Ukraine da ke kare yankin yayin da harin bindigogin manyan makamai da jiragen sama marasa matuka (drones) suka zama wani bangare na rayuwar yau da kullum.
Wannan barna na nuna irin halin da ake ciki a garuruwan da ke kan layin fadan yakin mai tsawon kilomita 1,200 a gabas da kudancin Ukraine.
KARANTA KUMA Harin Rasha kan wani wurin ajiye kayayyaki a Ukraine ya kashe mutane 38
“Ba na iya yin barci” in ji Iryna Litovchenko, mazauniyar garin mai shekaru 56 wacce ta ci gaba da zama a Druzhkivka.
Litovchenko ta ce “Gidana ya lalace gaba daya, tamkar bai taba kasancewa ba. Akwai abubuwa masu kyau da yawa a ciki komai yana nan da yawa. Amma a lokaci guda kurum sai ga shi komai ya bace tamkar babu komai da ya rage.”
Druzhkivka na daya daga cikin jerin garuruwa masu muhimmancin dabarun soja da ake kira “layin katangar tsaro” na Ukraine wuraren da sojojin Rasha ke kokarin kutsawa ciki yayin da Moscow ke neman mallake yankin Donbas baki daya.Duk da ci gaba da fafatawar da ake yi da sojojin Ukraine na ci gaba da kare yankin fiye da shekaru hudu bayan da Rasha ta kaddamar da cikakken farmakin mamaye kasar.
Jiragen sama marasa matuka (drones) na kara zama barazana ga fararen hula da sojoji inda aka shimfida rukunin kariya na musamman a kan wasu hanyoyi domin rage hadarin hare-hare.
Zoya, wata mazauniyar yankin mai shekaru 63 da ke sayar da kayan abinci a wajen wani shagon kasuwa da aka lalata ta bayyana cewa ta kuduri aniyar ci gaba da zama a wurin duk da hadarin da ke tattare da hakan.
Ta ce “Na san bam na iya fadowa ta sama har in rasa raina. Na fahimci hakan sarai. Abin yana karya zuciya.
“Yana sa in ji tamkar zan yi kuka. A nan aka haife ni a nan na girma. Kawai dai ban san me zan ce ba. Garinmu ya lalace.”
Reuters/Ladan Nasidi.



