Afirka

Sojojin Nijar Sun Fafata Da Masu Zanga-Zanga Kusa Daa Fillin Jirgin Saman Babban Birnin Kasar

Safina Umar Farouk.

Hukumomin sojin Nijar a ranar Asabar sun ce suna “sake samun iko a hankali” bayan da aka ruwaito cewa masu bore sun yi garkuwa da sojoji a wani sansanin soja kusa da babban birnin Niamey sannan suka yi harbi da bindiga.

A cikin wata sanarwa da aka karanta a talabijin na gwamnati kuma Ministan Tsaro Janar Salifou Mody ya sanya wa hannu hukumomi sun bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da ayyukansu na yau da kullun.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa manema labarai cewa “masu bore daga cikin sojojin” sun yi yunkurin shiga fadar shugaban kasa da ke Niamey amma masu gadin shugaban kasa sun kore su. An ruwaito cewa har yanzu ana ci gaba da harbe-harbe a kusa da fadar.

Mazauna yankin sun ba da rahoton jin karar harbe-harbe mai tsanani a cikin dare a sassa da dama na babban birnin kasar musamman kusa da fadar shugaban kasa da filin jirgin sama wanda ke dauke da wani babban sansanin soja.

Telebijin na gwamnati ba ya aiki sama da awa daya kafin a ci gaba da watsa shirye-shirye da misalin karfe 10 na safe agogon yankin.

Yanayin ya ci gaba da tabarbarewa, inda jami’an tsaro ke aiki don dawo da cikakken iko a yankunan da abin ya shafa.

 

 

 

Africanews/Safina Umar Farouk.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button