Gwamnatocin Libya Masu Hamayya Da Juna Sun Amince Da Lokacin Zabe

Bangarorin gwamnatoci masu hamayya a Libya sun amince su gudanar da zabe a cikin shekaru biyu masu zuwa domin sake hada kan kasar.
Bayan watanni ana tattaunawa tare da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da wakilan hukumomin gabas da yammacin Libya wadanda aka fi sani da Kwamitin 4+4 sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya a ranar Lahadi.
KARANTA KUMA: An gano gawarwakin bakin haure a hamadar Libya
Yarjejeniyar na da nufin sake fasalin hukumar zaben kasar da kuma warware sabanin da ake da shi kan dokokin zabe.
Mataimakin Shugaban Majalisar Shugabancin Libya Moussa Al-Koni ya ce yarjejeniyar za ta iya taimakawa kasar wajen kawo karshen rarrabuwar kawuna ta fuskar siyasa.
“Kasancewarmu a nan yau na nuna goyon baya ne ga wata dama ta siyasa da dole ne a kare ta tare da gina ta.”
Ya kara da cewa “Dama ce da za ta kai Libya matakin tafiyar da batun rarrabuwar kawuna tare da sauya yanayin daga jira kawai a yi zabe zuwa daukar matakan da za su haifar da ci gaba na zahiri wajen cimma hakan.”
Abdul Rahman Al-Abbar mamba a Kwamitin 4+4 mai wakiltar gwamnatin gabas, shi ma ya nuna gamsuwarsa da yarjejeniyar.
“A yau, a wannan muhimmiyar tattaunawa, tare da rattaba hannu kan sakamakon da aka cimma wannan shi ne kololuwar aikin da wasu mutane suka gudanar cikin kishin kasa na gaskiya.”
Libya ta shiga cikin rudani da rashin kwanciyar hankali bayan an hambarar da shugaba mai dadewa kan mulki Moammar Gadhafi a shekarar 2011.
Tun daga lokacin kasar ta kasu kashi biyu tsakanin gwamnatoci biyu: Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Abdulhamid Dbeibah (wadda kasashen duniya ke amincewa da ita) a yamma da kuma Gwamnatin Kwanciyar Hankalin Kasa ta Khalifa Haftar (mai hamayya da ita) a gabas.
An fara tattaunawar da nufin sake hada kan kasar ne a karshen shekarar da ta gabata, bayan bangarorin biyu sun bukaci Pakistan ta shiga tsakani domin sulhu.
AFRICANEWS/Ladan Nasidi.



