Siyasa

APC Za Ta Tabbatar Da Sake Zaben Tinubu – Yari

Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Abdul’aziz Yari ya bayyana cewa jam’iyyar za ta cika alkawuran da ta yi a yakin neman zabe tare da yin aiki tukuru domin ganin an sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.

Yari ya yi wannan jawabi ne a Abuja bayan da magoya bayansa suka yi masa tarba ta musamman sakamakon dawowarsa daga wata tafiya ta kasashen waje.

Da aka tambaye shi yadda yake ji game da nadin da aka yi masa da kuma tarbar da magoya bayansa suka yi masa a fadin kasar Yari ya bayyana cewa yana jin alfahari da amincewar da Shugaba Tinubu ya nuna a gare shi.

“Ina jin alfahari. Ina jin alfahari da wannan amincewa da Shugaban Kasa ya yi mini. Kuma In sha Allahu zan yi iya bakin kokarina wajen ganin mun cimma nasara” in ji shi.

Ya ce bukukuwan da ake yi a yanzu farko ne kawai, inda ya jaddada cewa hakikanin murnar za ta zo ne bayan zaben 2027. “A yau komai na murna ne. Amma hakikanin murnar za ta zo ne a watan Janairu idan mun cimma nasarar da ake bukata.”

Yari ya yi kira ga magoya bayan APC da su hada kai wajen goyon bayan Tinubu tare da yin addu’ar samun nasarar kwamitin yakin neman zaben.

 

KARANTA KUMA: Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa ya nemi afuwar ‘ya’yan jam’iyyar na jihar Oyo da ke da korafi

“Wannan lokaci ne da ya kamata mu haɗu domin tabbatar da cewa muna yin abu ɗaya. Wannan abu ɗaya shine Bola Tinubu.” Yari ya jaddada.

Dangane da abin da ‘yan Najeriya ya kamata su zata daga APC Yari ya yi alƙawarin cewa jam’iyyar za ta ci gaba da bin manufofinta da alkawuran yakin neman zaɓe.

“Duk abin da muka faɗa a lokacin kamfen mu cika manufofinmu mu cika alƙawarinmu domin zaɓen ba na yau ba ne.”

Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya ce APC ta yi imanin cewa Tinubu zai sake samun wa’adi a kan mulki a 2027.

Yari ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa APC za ta ci gaba da kasancewa jam’iyyar da ke mulki a Najeriya bayan wa’adin Tinubu na biyu.

“Muna addu’ar jam’iyyar ta ci gaba da mulki bayan Tinubu a matsayin jam’iyyar da za ta jagoranci ƙasar.”

Ya ce jajircewar jam’iyyar na cika alkawarinta zai zama babban abin da zai sa ta yi kamfen ɗinta yayin da yake addu’ar Allah ya ba wa Shugaba Tinubu hikimar jagoranci ƙasar da kuma cika alkawuran da aka yi wa ‘yan Najeriya.

 

 

LADAN NASIDI.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button