Taiwan Ta Gudanar Da Zabe A Yayin Da Matsin Lamba Na Soja Da Na Siyasa Daga Kasar Sin Ke Karuwa

Masu jefa ƙuri’a a Taiwan sun je rumfunan zaɓe ranar Asabar don zaɓar magajin gari da shugabannin gundumomi a birane da gundumomi 22 na tsibirin inda matsalolin yankin suka mamaye kamfen duk da ƙaruwar matsin lamba na soja da siyasa daga Chana.
Ko da yake zaɓen ya fi mayar da hankali kan harkokin sufuri muhalli da sauran matsalolin cikin gida Beijing ta ci gaba da sukar Jam’iyyar Democrat Progressive Party (DPP) mai mulki musamman ɗan takarar magajin garin Taipei Puma Shen.
Chana wadda ke iƙirarin Taiwan a matsayin ƙasarta ta zargi Shen da “ɓarna” kuma ta ayyana shi a matsayin wanda ‘yan sandan Chana ke nema. Duk da haka Shen ya shaida wa Reuters cewa duk wanda ya lashe zaɓen Taipei zai wakilci nasara ga dimokuraɗiyya idan aka fuskanci matsin lamba daga Chana..
Kafafen watsa labarai na gwamnatin Chana sun ƙara kai hare-hare a kansa a ranar Juma’a suna zarginsa da karɓar kuɗaɗen Amurka da kuma zargin cewa Washington tana “Amfani da hanyoyi na ɓoye don tsoma baki sosai” a zaɓen.
Babban mai ƙalubalantar Shen shine Magajin Garin Taipei Chiang Wan-an na jam’iyyar adawa ta Kuomintang (KMT) wadda a al’ada ta fi son kusanci da Beijing.
KARANTA KUMA: Zaɓen Yankin Taiwan Ya Ja Hankalin Chana
A halin yanzu ma’aikatar tsaron Taiwan ta ba da rahoton gano jiragen saman soja na China 33 da jiragen yaƙi takwas a kusa da tsibirin cikin awanni 24 da suka gabata kafin safiyar Asabar.
Alex Huang mai ba da shawara ga Majalisar Tsaron Ƙasa ta Taiwan ya ce China ta kunna dandamalin farfagandarta da Ofishin Harkokin Taiwan a daren Juma’a wanda ke nuna “jajibirin zaɓe”.
Zaɓen Shugaban Ƙasa/Majalisar Dokoki
Ana kuma sa ran zaɓen ƙananan hukumomi zai tsara dabarun siyasa kafin zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisa na Taiwan da aka shirya yi a farkon 2028.
A zaɓen ƙananan hukumomi da ya gabata a 2022 KMT ta sami birane da gundumomi 14 idan aka kwatanta da biyar da DPP ta lashe yayin da sauran jam’iyyu da masu zaman kansu suka karɓi sauran ukun.
Ana sa ran Shugaba Lai Ching-te zai nemi wa’adi na biyu yayin da KMT ba ta sanar da ɗan takararta ba tukuna. Tsohon ɗan jarida kuma magajin garin Taichung Lu Shiow-yen ana ɗaukarsa a matsayin wanda zai iya tsayawa takara.
Beijing ta ki tattaunawa da Lai wanda ta sanya wa lakabin “mai son ballewa” yayin da shugaban Taiwan ya nanata cewa mutanen tsibirin ne kawai ke da ikon yanke hukunci kan makomarsu.
Baya ga Taipei sauran zabukan da ake sa ido sosai a kansu sun hada da New Taipei birnin da ya fi kowa yawan jama’a a tsibirin da kuma Kaohsiung wanda a al’adance yake zama mazaunin karfin jam’iyyar DPP inda jam’iyyar KMT ta kara kaimi wajen gudanar da yakin neman zabenta.



