Siyasa

Uwargidan Shugaban Kasa Ta Nemi Goyon Bayan Mata Domin Sake Zaben Shugaba Tinubu

Uwargidan Shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta yi kira ga mata a yankin Kudu-maso-Kudu da su goyi bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Delta Sheriff Oborevwori a shekarar 2027.

Ta yi wannan kiran ne a yayin kaddamar da gangamin yakin neman zaben mata na jam’iyyar APC a yankin Kudu-maso-Kudu wanda aka gudanar a birnin Warri na Jihar Delta.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa shirin ‘Renewed Hope Agenda’ (Ajandar Sabon Fatan) na gwamnatin Shugaba Tinubu ya ba da fifiko ga karfafa tattalin arzikin mata da kuma samar da kariya ta zamantakewa a gare su ta hanyar matakai da shirye-shirye daban-daban.

KARANTA KUMA: Uwargidan Shugaban Kasa Ta Tara Mata A Yankin Arewa-Maso-Yamma Gabanin Zabe

Ta yi nuni da tsarin bayar da lamunin karatu ga dalibai ayyukan raya ababen more rayuwa ciki har da babbar hanyar da ke bi ta bakin teku daga Legas zuwa Calabar da tallafin kudi ga ‘yan kasuwa da sauran shirye-shiryen da nufin inganta rayuwar al’umma.

Ta yi kira ga mata da su zabi ‘yan takarar jam’iyyar APC musamman Shugaba Tinubu da Gwamna Oborevwori wadanda ta bayyana a matsayin shugabanni da suka sadaukar da kansu wajen kula da walwalarsu.

“Ba na damuwa da duk abin da za su kira shi matukar dai mata na suna cikin farin ciki da wadata” in ji ta.

Da take bayyana taron a matsayin wani dawowar gida Uwargidan Shugaban Kasa ta tabbatar wa mata cewa ayyukan ci gaba da ake gudanarwa a fadin Jihar Delta da kuma kasar za su ci gaba da wuce tsammaninsu idan aka sake zabar shugabannin biyu.

Ta kuma kaddamar da wani shiri na karfafa gwiwa wanda ta hanyarsa mata kimanin 1,000 suka sami injinan daskarewa injinan dinki injinan nika na’urorin busar da gashi kiosks da ƙananan motoci da sauransu.

Tun da farko Misis Tinubu ta kaddamar da titin Warri-Ode-Itsekiri mai tsawon kilomita 20.95 wanda ke dauke da gadoji da kuma manyan hanyoyi 15 da ke makwabtaka da ita a yankin karamar hukumar Warri ta Kudu.

Ta ketare kogin daga Ifie zuwa Ode-Itsekiri domin kaddamar da hanyar wacce Gwamnatin Jihar Delta ta gina.

Uwargidan Shugaban Kasa ta bayyana aikin a matsayin misalin ci gaban ababen more rayuwa da ake sa ran gani yayin da Najeriya ke sauyawa daga matakan gyaran tattalin arziki zuwa samun wadata.

Gwamna Sheriff Oborevwori ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa samar da karin albarkatu ga gwamnatocin jihohi inda ya ce hanyar ta nuna kudurin gwamnatinsa na hada al’ummomi domin samun ci gaba mai sauri.

Aikin hanyar ya dauki tsawon kimanin shekaru 18 ba tare da an kammala shi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button