Wasanni

CAF Ta Gabatar Da Mataimakin Alƙalin Wasa Na Bidiyo Don Gasar Wasanni Tsakanin Kugiyoyi

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) za ta gabatar da tsarin amfani da na’urar taimaka wa alkalan wasa ta bidiyo (VAR) a dukkan wasannin matakin rukuni na gasar Champions League da Confederation Cup na kakar 2026/2027.

Wannan shi ne karo na farko da za a yi amfani da VAR a matakin rukuni na gasannin kulob-kulob na CAF a baya ana amfani da ita ne kawai a matakan fitar da wanda ya yi nasara (knockout stages) na gasar Champions League da Confederation Cup.

A matakin rukuni na gasar Confederation Cup gabatar da VAR zai ba da ƙarin tallafi ga jami’an wasa tare da bayar da gudummawa mai muhimmanci wajen sanya matsayin gudanar da wasanni da aikin alkalan wasa su kasance daga cikin mafi kyau a duniya.

A karkashin jagorancin Shugaban CAF Patrice Motsepe hukumar ta ba da fifiko ga zuba jari a fannin ababen more rayuwa na kwallon kafa fasaha bunkasa aikin alkalan wasa, da kuma inganta gasanninta zuwa matakin kwararru.

KARANTA KARIN BAYANI: CAF Ta Bayyana Sunayen ‘Yan Wasa Biyar Da Suka Kai Matakin Karshe Na Kyautar Gwarzon Dan Wasan Maza

Wannan ci gaba ya samu ne sakamakon shirin ‘CAF VAR Academy’ wanda ya samar da fasahar tare da horar da kwararrun jami’an wasa na VAR (VMOs) a dukkan yankuna shida na kungiyoyin kwallon kafa na Afirka (CAF Zonal Unions).

Ana gudanar da horo na musamman kan VAR a matakin yankuna da kuma matakin nahiya wanda ke taimakawa wajen samar da karin kwararrun jami’an VAR masu gogewa. Kasancewar wadannan kwararrun jami’ai yana karfafa daidaito wajen yanke hukunci tare da gina amincewa ga aikin alkalan wasa na Afirka da kuma kwallon kafar Afirka baki daya.

CAF ta ci gaba da fadada amfani da VAR a manyan gasanninta wadanda suka hada da gasar cin kofin Afirka (AFCON) gasar cin kofin Afirka na mata (WAFCON) da kuma gasannin kulob-kulob na CAF.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button