Pakistan Ta Tura Sojoji Zuwa Saudiyya Bayan Tattaunawa Kan Harkokin Tsaro

Rundunar sojan Pakistan ta bayyana cewa kasar ta tura dakarunta zuwa kasar Saudiyya biyo bayan wani babban taro na “Kawancen Tsaro na Makka” (Mecca Alliance for Defence) da aka gudanar a birnin Islamabad.
A cewar rundunar sojan Pakistan an sanar da tura dakarun ne a ranar Asabar kwana guda bayan kammala taron.
Rundunar ta ce matakin ya nuna irin “kudurorin da Pakistan ba ta sauya zani a kansu ba na kare tsaro ikon mallakar kasa da kuma yankunan kasar” Saudiyya.
KARANTA KUMA: Pakistan Saudiyya Da Turkiyya Za Su Tattauna Kan Tsaron Juna
Dakarun za su gudanar da ayyukansu a cikin kasar Saudiyya bisa yarjejeniyoyin da aka cimma da kuma tsarin hadin gwiwar tsaro da ke akwai.
Matakin yana da nufin kara karfafa karfin tsaron kasar Saudiyya a daidai lokacin da ake fuskantar sabbin kalubalen tsaro.
Wannan ya biyo bayan taro na biyu na Kwamitin Siyasa da Tsaro na “Kawancen Tsaro na Makka” wanda aka gudanar a ranar Juma’a a Islamabad tare da halartar manyan jami’an gwamnati da na soji daga kasashen Pakista Saudiyya da Turkiyya.



