Jihar Ebonyi: Zaben Gwaji Na INEC Ya Gudana Cikin Lumana Tare Da Fitowar Masu Kada Kuri’a

Atisayen tantance masu jefa ƙuri’a da kuma zaɓen gwaji wanda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta shirya ya gudana cikin kwanciyar hankali tare da fitowar masu son jefa ƙuri’a mai gamsarwa a ƙananan hukumomin Abakaliki Ezza North da Ezza South na jihar Ebonyi.
Ayyukan sun gudana cikin lumana a dukkan ƙananan hukumomin uku inda masu son jefa ƙuri’a suka fito domin shiga cikin tsarin zaɓen na gwaji.
A cibiyar gwajin da ke rumfar zaɓe mai lamba 003 a unguwar Izzi Unuphu Ward 10 masu zaɓen da suka yi rajista sun riga sun isa wurin domin shiga cikin atisayen.
KARANTA KUMA: INEC Ta Gudanar Da Zaɓen Gwaji A Rumfunan Zaɓe 450 A Jihar Kebbi
An gudanar da atisayen a cibiyoyin gwaji da aka ware a faɗin jihar.
Kwamishiniyar Zaɓe ta INEC a jihar Ebonyi Misis Pauline Onyeka wacce ta sanya ido kan yadda abubuwa ke gudana a rumfar zaɓe ta Igbudu Eka da ke ƙaramar hukumar Ezza North ta tabbatar da cewa atisayen ya yi nasara.
Onyeka ta ce “Wannan wani ɓangare ne na shirye-shiryen INEC domin babban zaɓen shekarar 2027 kuma an yi shi ne domin gwada ingancin aikin na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS duba tsarin tantancewar da kuma tantance yadda ake tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura.”
Ana gudanar da wannan atisaye na gwaji a faɗin ƙasar a wasu rumfunan zaɓe da aka zaɓa a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya domin auna shirye-shiryen hukumar ta fuskar fasaha da gudanarwa kafin lokacin zaɓen.
Ana sa ran INEC za ta yi amfani da bayanan da aka samu daga wannan atisaye domin gano matsalolin fasaha da na tsare-tsare tare da yin gyare-gyaren da suka dace kafin babban zaɓen 2027.
Jami’an da ke kula da rumfunan zaɓen waɗanda suka haɗa da Onu John Egbuhuzor Ahamefula da Godwin Nwokocha sun tabbatar da cewa zaɓen gwajin ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Sai dai ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na majalisar dokokin jihar mai wakiltar Ezza North West Nwafor Joseph ya bayyana cewa an samu ƙarancin fitowar masu zaɓe a wasu yankuna na mazabar yayin gudanar da atisayen.



