Hukumar Zabe INEC Ta Gudanar Da Zaben Gwaji A Legas

Mazauna Jihar Legas wadda ita ce cibiyar kasuwanci ta Najeriya sun shiga cikin atisayen gwajin tantance masu zabe da kada kuri’a wanda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shirya gabanin babban zaben shekarar 2027.
A yayin atisayen da aka gudanar a ranar Asabar masu zabe da suka cika sharudda daga rumfunan zabe guda biyu a kowace mazabar zabe sun halarci wannan gwajin zaben.

Gidan Rediyon Muryar Nigeriya (VON) ya bayar da rahoton cewa mazauna yankunan da aka ware domin kada kuri’a sun fito domin gudanar da ayyukansu na zabe.
KARANTA KUMA: Zaben Gwaji Na INEC Ya Gudana Cikin Kwanciyar Hankali A Jihar Ebonyi
Shugaban Karamar Hukumar Oshodi-Isolo Kehinde Oloyede ya yi kira ga masu zabe da su dauki wannan zaben gwaji a matsayin damar auna shirin hukumar INEC na gudanar da babban zaben shekarar 2027.
Zaben gwajin ya kammala da misalin karfe 2:30 na rana a ranar Asabar kuma an tsara shi ne domin tantance shirin na’urar tantance masu zabe ta BVAS da gwada yadda ake tura sakamakon zabe kai tsaye zuwa shafin yanar gizo na INEC (Irev) tare da gano matsalolin fasaha ko na tsare-tsare da ka iya tasowa kafin babban zaben.



