Duniya

Sojojin Amurka Sun Tare Jirage Marasa Matuka Guda Shida Kusa Da Sansanin Sojin Sama Na Birtaniya

Rahotanni sun ce sojojin Amurka sun dakile jiragen sama marasa matuki guda shida da suka kusanci sansanin sojin saman RAF Lakenheath na Burtaniya a farkon wannan watan.

Amurka ta tura fasahar hana amfani da jiragen sama marasa matuki don dakile jiragen sama marasa matuki amma rahotanni sun ce babu wani ma’aikacin Birtaniya ko na Amurka da ya kwato jiragen.

KARANTA KUMA: Sojojin Amurka Sun Nakasa Jirgin Ruwa Saboda Yunkurin Katange Iran

Shugaba Donald Trump ya ce a watan da ya gabata cewa barazanar da ke da alaka da Iran ce ta sa aka cire jiragen bama-bamai na Amurka B-1 daga RAF Fairford wani sansanin jiragen saman Birtaniya da sojojin saman Amurka ke amfani da shi a lokacin wani lamari da ya faru a watan satunba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button