Fashewa A Pakistan Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 11 Tare Da Jikkata Wasu 30
Hukumar agajin gaggawa ta ‘Rescue 1122’ ta tabbatar da cewa mutane akalla 11 ne suka mutu yayin da wasu 30 suka jikkata sakamakon wani fashewa a Dera Ismail Khan yankin arewa maso yammacin Pakistan a ranar Asabar.
A cewar sanarwar da hukumar agajin ta fitar fashewar ta faru ne kusa da yankin Aman Mela a yankin Darazinda na gundumar.
Kungiyoyin agaji daga tashar Darazinda sun isa wurin da lamarin ya faru inda suka bai wa wadanda suka jikkata kulawar likita tare da kai su asibiti.
KARANTA KUMA: Fashewar Masallaci a Pakistan: Adadin Wadanda suka Mutu ya Kai 92
Kungiyar Tehreek-e-Taliban Pakistan ce ta dauki alhakin kai harin.
Yankin Dera Ismail Khan wanda ke lardin Khyber Pakhtunkhwa kusa da iyakar Pakistan da Afghanistan ya sha fuskantar hare-haren ‘yan bindiga masu tsatsauran ra’ayin Islama akai-akai wadanda galibi ke kai hari kan ‘yan sanda da jami’an tsaro.
An ci gaba da samun matsalolin tsaro a gundumar a wannan watan ciki har da hare-haren da kungiyar Taliban ta Pakistan ke da hannu a cikinsu.



