Tsohon Firayim Ministan Guinea Touré Ya Rasu

Tsohon Firayim Minista kuma babban jigon ‘yan adawa a kasar Guinea Sidya Touré ya rasu yana da shekaru 81 a duniya.
Touré ya kasance yana jagorantar daya daga cikin manyan jam’iyyun adawa na kasar, wato Union of Republican Forces (UFR) yayin da yake gudun hijira a kasar Ivory Coast.
Jam’iyyar UFR na daya daga cikin jam’iyyun siyasa 40 da aka soke a watan Maris a cikin wani mataki mai tsauri na takaita ‘yancin jama’a karkashin jagorancin shugaba mai karfin iko na kasar Mamady Doumbouya.
Wata majiya mai kusanci da iyalin marigayin ta bayyana cewa Touré ya rasu ne a ranar Juma’a a birnin Paris bayan shafe shekaru da dama yana taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasa da rayuwar jama’ar Guinea.
Majiyoyin wadanda suka bukaci a boye sunayensu saboda dalilai na tsaro sun ce an kwantar da shi a Asibitin Amurka da ke Paris (American Hospital of Paris) na tsawon makonni biyu bayan ya yi rashin lafiya a birnin Abidjan.
Touré ya zauna a Abidjan tun bayan barin kasar Guinea sakamakon juyin mulkin soji na watan Satumbar 2021 wanda ya kawo Doumbouya kan karagar mulki.
Daga baya, an zabi Doumbouya a matsayin shugaban kasar ta Yammacin Afirka a watan Disambar bara a zaben da aka ware manyan jam’iyyun adawa ciki har da UFR da sauran manyan jam’iyyun adawa biyu na kasar wato UFDG da RPG.
Shugaban jam’iyyar UFDG Cellou Dalein Diallo wanda shi ma ke zaune a gudun hijira ya bayyana bakin cikinsa game da rashin “aboki kuma abokin gwagwarmaya” domin kasar Guinea, a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Touré ya yi tarayya wajen burin ganin an canza fasalin “kasarmu tare da dukkan dumbin damammakin da take da su zuwa kasa mai bunkasar tattalin arziki da ke tafiya bisa ka’idojin dimokuradiyya da bin doka da oda.”
Shugaban kasar Guinea Lansana Conte wanda ya yi mulki tsakanin shekarun 1984 da 2008 ya nada Touré a matsayin Firayim Minista a watan Yulin 1996 mukamin da ya rike har zuwa watan Maris na 1999.
Lokacin da ya rike mukamin Firayim Minista ya kasance mai cike da sauye-sauye a fannin gudanarwa da tattalin arziki tare da kokarin karfafa dangantakar Guinea da cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya.
Bayan ya bar gwamnati Touré ya zama shugaban jam’iyyar UFR a shekarar 2000. A hankali ya zama babban jigo wajen nuna adawa ga Conte da kuma gwamnatocin da suka biyo bayansa.
Touré ya tsaya takarar shugaban kasa a matsayin dan takarar jam’iyyar UFR a shekarun 2010 da 2015 inda ya sha kashi a dukkan lokutan biyu.
An haife shi a shekarar 1945 a kasar Ivory Coast inda kuma ya yi wani bangare na aikinsa musamman a fannin gudanar da harkokin tattalin arziki da kudi.
Tsohon shugaban kasa Alpha Conde—wanda Touré ya yi aiki a karkashinsa duk da cewa sun taba samun sabani a wasu lokuta—ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, abin takaici ne matuka yadda mutumin da ya ba kasarsa gudunmawa mai yawa ya tsinci kansa cikin halin wahalar rayuwa a gudun hijira a karshen rayuwarsa.
Firayim Ministan Guinea na yanzu Amadou Oury Bah ya bayyana Touré a wani sako da ya wallafa a shafin X a matsayin “mai kawo sauyi mai duba gaskiyar al’amura” da kuma “fitaccen mutum a fagen siyasar Guinea na tsawon shekaru talatin.“



