Duniya

Shugaba Trump Ya Yi Hasashen Yarjejeniyar Amurka Da Cuba Ba Tare Da Matakin Soja Ba

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana sa ran Amurka da Cuba za su cimma yarjejeniya inda ya jaddada cewa ba za a bukaci daukar matakin soja a kan kasar ba.

“Ina ganin cewa Amurka da Cuba za su cimma yarjejeniya. Ba na tunanin za mu bukaci amfani da sojoji” in ji Shugaba Trump yayin da yake zantawa da manema labarai a Fadar White House ranar Asabar.

Ya bayyana hakan ne kafin ya tafi jihar Tennessee, yayin da gwamnatinsa ke ci gaba da matsa lamba kan gwamnatin Cuba.

Gwamnatin Amurka ta bayyana a fili cewa manufarta ita ce sauya gwamnatin Cuba. Matakin hana shigo da man fetur da Washington ta dauka a farkon wannan shekarar ya kara jefa kasar cikin mawuyacin hali yayin da take fuskantar karancin man fetur da katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar kayayyakin more rayuwa.

Shugaba Trump ya ce: “Muna son taimaka wa Cuba… Muna son bude kofar Cuba ga mutanenmu.”

KARANTA KUMA: Amurka ta sanya takunkumi kan hukumomi ko kamfanoni 11 na Cuba

A cikin jawabin da ya yi a gaban Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata Shugaba Trump ya kwatanta Cuba a matsayin kasa da ta gaza inda ya ce “yanci zai zo” ga kasar. Tawagar wakilan Cuba ta fice daga zauren taron yayin da yake jawabi.

Daga baya ranar Asabar Ministan Harkokin Wajen Cuba Bruno Rodriguez ya bayyana cewa Cuba a shirye take ta tattauna da Amurka ba tare da ya yi tsokaci kai tsaye kan kalaman Shugaba Trump ba.

“A shirye muke mu gudanar da harkokin kasuwanci da kamfanonin Amurka kamar yadda muke yi da sauran kasashe” in ji Rodriguez yayin da yake kakkausar suka kan takunkumin kasuwanci da Amurka ta dade tana kakaba wa Cuba.

Amurka ta ci gaba da aiwatar da wannan takunkumi na tsawon sama da shekaru 60 yayin da gwamnatin Shugaba Trump ta kara matsa lamba kan Havana a ‘yan watannin nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button