Fitattun LabaraiNajeriya

Shugaba Tinubu Ya Yi Maraba Da Karuwar GDP Da kashi 4.43% Tare Da Tabbacin Samun Tattalin Arziki Mai Karfi

Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ‘yan Najeriya tabbacin samun ingantaccen yanayin tattalin arziki biyo bayan karuwar kashi 4.43 cikin dari da aka samu a Jimlar Kayayyaki da Ayyuka da ake samarwa a kasar (GDP) a zango na biyu na shekarar 2026.

Da yake mayar da martani a ranar Litinin kan sabon rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) wanda ya nuna cewa tattalin arzikin ya samu karuwar kashi 4.43 cikin dari a zango na biyu na 2026, idan aka kwatanta da kashi 4.23 cikin dari a irin wannan lokacin na shekarar 2025  Shugaba Tinubu ya bayyana hakan a matsayin karin shaida ta ci gaban da ake samu a karkashin gwamnatinsa.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu, Shugaban ya ce rahoton ya zo ne a lokacin da ya dace matuka musamman ganin yadda ‘yan adawa ke ci gaba da raina tasirin gyare-gyaren da gwamnatinsa ta aiwatar tun watan Mayun 2023 tare da yin alkawarin soke wasu daga cikin manufofin idan aka zabe su.

 

KARANTA KUMA: Najeriya na da burin cimma GDP na Naira Tiriliyan 530 nan da watan Disamba

Shugaba Tinubu ya ce gyare-gyaren sun taimaka wajen daidaita tattalin arziki tare da shimfida harsashin samun ci gaba mai dorewa da wadata.

“A cikin shekaru uku da suka gabata, mun yi kokarin daukar matakai masu wahala ta hanyar aiwatar da gyare-gyaren da suka dace domin daidaita tattalin arziki. Yanzu tattalin arzikin ya daidaita, kuma mun shimfida harsashin kasa mai wadata. Ba mu aiwatar da gyare-gyaren domin haifar da kalubale ba sai dai domin tabbatar da cewa wadatar tattalin arziki ta isa ga dukkan al’ummarmu” in ji shi.

Ya ambaci ingantattun asusun ajiyar waje, rarar ciniki, karuwar samar da mai, sabunta kwarin gwiwar masu zuba jari da kuma karuwar ci gaban ababen more rayuwa a matsayin shaida cewa Ajandar Sabunta Fata tana samar da sakamako.

“Sakamakon kokarin ya bayyana ga kowa Ajandar Sabunta Fata tana aiki. Saboda wadannan tsauraran shawarwari a yau Najeriya tana da rarar ciniki. Asusun ajiyarmu na kasashen waje ya kai kololuwar da ta kai a cikin shekaru 17. Matsayin basussukanmu ya karu da dama.

Muna gina hanyoyi da layin dogo da manyan hanyoyi wadanda zasu dade na tsawon lokaci. Masu zuba jari da suka tafi suna dawowa. Samar da mai da iskar gas yana karuwa.

“Kuma a jami’o’inmu  a karon farko cikin dogon lokaci  babu yajin aiki. Yaranmu suna cikin aji. Ta hanyar NELFUND lamunin ɗalibai yana sanya ilimi ya isa ga kowa, yayin da ake samar da lamuni mai araha ga ma’aikatan gwamnati ta hanyar Creditcorp.”

Shugaban kasar ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati za ta kara himma wajen rage tsadar rayuwa ta hanyar sufuri mai rahusa da karuwar samar da abinci da shirye-shiryen agaji da aka yi niyya.

 

 

 

Ladan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button