Afirka

Guinea-Bissau Ta Amince Da Sabon Kundin Tsarin Mulki Gabanin Kada Kuri’a

 

Guinea-Bissau ta amince da sabon kundin tsarin mulki da zai fadada ikon shugaban kasa da kuma sauya dokokin zabe kafin zaben shugaban kasa da aka shirya yi a watan Disamba.

Kashi 70 cikin 100 na masu kada kuri’a sun amince da kuri’ar raba gardama da aka gudanar a ranar Lahadi yayin da kashi 30 cikin 100 suka kaɗa ƙuri’ar kin amincewa da gyare-gyaren.

A cewar Hukumar Zabe ta Kasa mutane 544,060 ne suka halarci kuri’ar raba gardama wadanda ke wakiltar kusan kashi 60 cikin 100 na masu kada kuri’a da suka yi rijista.

Sabon kundin tsarin mulki ya bai wa shugaban kasa ikon nadawa da korar firaminista da majalisar ministoci da kirkiro ko soke ma’aikatu da kuma rusa majalisar dokoki idan akwai rikicin siyasa mai tsanani.

A karkashin kundin tsarin mulkin da ke akwai majalisar dokoki ta nada firaminista wanda daga nan zai kafa majalisar ministoci.

Gyaran ya bai wa gwamnatin soja wadda ta kwace mulki a wani juyin mulki a watan Nuwamban da ya gabata da tsarin da zai sake fasalin tsarin siyasar kasar kafin zaben shugaban kasa na watan Disamba.

KARANTA KUMA: Guinea-Bissau za ta gudanar da zaben raba gardama kan sauye-sauyen kundin tsarin mulki

Sai dai babban jam’iyyar adawa ta African Party for the Independence of Guinea and Cape Verde (PAIGC) ta kauracewa zaben raba gardamar inda ta yi ikirarin cewa tsarin bai kunshi isassun matakan kare siyasa da hukumomi ba.

Shugaban jam’iyyar PAIGC Domingos Simoes Pereira ya zargi masu goyon bayan zaben raba gardamar da yunkurin raunana tsarin dimokuradiyya hakan ya fito ne a cikin wani sakon bidiyo.

Ba a samu damar jin ta bakin mai magana da yawun gwamnatin sojin ba nan take.

Sabon kundin tsarin mulkin ya kuma rage yawan kujerun majalisar dokoki daga 102 zuwa 65 tare da rage yawan mazabun zabe daga 29 zuwa 12.

Har ila yau yana bukatar ‘yan takarar shugaban kasa su kasance sun zauna a Guinea-Bissau ba tare da katsewa ba na tsawon akalla shekaru biyar kafin su tsaya takara.

Wannan juyin mulki shi ne na tara da aka samu a yankunan Yamma da Tsakiyar Afirka cikin shekaru biyar lamarin da ya kara ta’azzara dogon tarihin rashin kwanciyar hankali na siyasa da kuma shiga tsakani na sojoji a Guinea-Bissau.

 

 

Reuters/Ladan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button