Shugaba Tinubu ya yi maraba da karuwar GDP da kashi 4.43% tare da ba da tabbacin samun tattalin arziki mai karfi

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tattalin arzikin kasar zai inganta bayan karuwar kashi 4.43 cikin 100 da aka samu a cikin GDP na kasar a kwata na biyu na shekarar 2026.
Da yake mayar da martani a ranar Litinin ga sabon rahoton da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar wanda ya nuna cewa tattalin arzikin kasar ya karu da kashi 4.43 cikin 100 a kwata na biyu na shekarar 2026 idan aka kwatanta da kashi 4.23 cikin 100 a daidai lokacin shekarar 2025 Shugaba Tinubu ya bayyana ci gaban a matsayin wani karin shaida na ci gaba a karkashin gwamnatinsa.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu Shugaban ya ce rahoton ya zo ne a wani muhimmin lokaci musamman yayin da ‘yan adawa ke ci gaba da rage tasirin gyare-gyaren gwamnatinsa tun daga watan Mayu na shekarar 2023 kuma ya yi alkawarin sauya wasu manufofi idan aka zabe shi.
KARANTA KUMA: Najeriya Ta Yi Nasarar Naira tiriliyan 530 a watan Disamba
Shugaba Tinubu ya ce gyare-gyaren sun taimaka wajen daidaita tattalin arziki tare da shimfida harsashin ci gaba da wadata mai dorewa.
“A cikin shekaru uku da suka gabata mun yi ƙoƙarin yin aiki tuƙuru ta hanyar aiwatar da gyare-gyaren da ake buƙata don daidaita tattalin arziki. Yanzu tattalin arzikin ya daidaita da kuma mun kafa harsashin gina ƙasa mai wadata. Ba mu yi gyare-gyaren don ƙirƙirar ƙalubale ba amma don tabbatar da cewa wadata ta isa ga dukkan mutanenmu” in ji shi.
Ya ambaci ingantattun asusun ajiyar waje da rarar ciniki da ƙaruwar samar da mai, sabunta kwarin gwiwar masu zuba jari da kuma ƙara haɓaka kayayyakin more rayuwa a matsayin shaida cewa Ajandar Sabunta Fata tana samar da sakamako.
Ladan Nasidi.


