Najeriya

Shugaba Tinubu: Binciken Kwararru Ya Tabbatar da Farfadowar Tattalin Arzikin Najeriya

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa karuwar kyakkyawan nazari kan yanayin tattalin arziki daga masana da kuma alamun ci gaba a fannin tattalin arziki na nuni da makoma mai kyau ga dukkan ‘yan Najeriya.

 

Shugaban wanda ya karbi bakuncin kwamitin gudanarwa da manyan jami’an kamfanin Nigerian Exchange Group a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis ya ce dukkan matakan gyare-gyaren sun yi daidai da ka’idojin duniya kuma sun taimaka wajen farfado da tattalin arziki tare da shimfida harsashin ci gaba mai dorewa na dogon lokaci.

 

Tawagar kamfanin Nigerian Exchange Group karkashin jagorancin Shugaban kwamitin gudanarwa Dr. Umaru Kwairanga da Babban Daraktan kamfanin Temi Popoola sun yi wa Shugaban bayani kan yadda kasuwar ta farfado daga darajar Naira tiriliyan 30 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 160 a halin yanzu.

 

A cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya fitar Shugaba Tinubu ya yaba wa tawagar kula da harkokin tattalin arziki wacce ta kunshi Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da daidaita harkokin tattalin arziki Taiwo Oyedele Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa Atiku Bagudu Gwamnan Babban Bankin Najeriya Yemi Cardoso da Shugaban Hukumar Tara Kudin Shiga ta Kasa (FIRS) Dr. Zacch Adedeji saboda hangen nesa sadaukarwa da kuma kwazon da suka nuna.

“Ina ganin yanayin farin ciki a wannan zauren. Abin da zan iya yi kawai shi ne in taya ku murna baki daya a yau. Abin farin ciki ne samun irin wannan martani. Lokacin da muka karbi ragamar mulkiyanayin yana da matukar wahala. Dole ta sa na yi wa kaina bayani tare da tunawa da tushena domin na amince da dukiyar da basussukan da wanda ya gabace ni ya bari.

 

“Ni na nemi wannan aiki kuma dole ne in yi shi. Kuma abokin aikina mai kwarewa wanda muka yi nazari da tunani tare a lokuta masu muhimmanci shi ne Yemi Cardoso wanda na nada a matsayin shugaban Babban Bankin Najeriya (CBN).

 

“Na samu abokin aiki a cikin shugaban CBN Yemi Cardoso. Mun tsinci kanmu a yanayi mara kyau dangane da manufofin kudi da kuma ajiyar kudaden kasa. An buga kudi har Naira tiriliyan 30, kuma akwai basussuka da dama. Ina yi maka godiya sosai Yemi Cardoso.

“Dangane da sauran tawagar, muna da nauyin da ya rataya a wuyanmu ga kasa tare da yakinin cewa za mu iya cimma wannan buri. Najeriya za ta iya gina kasa mai wadata da kanta. Idan kasuwar hannun jari tana tafiya yadda ya kamata to hakan na nufin muna samun nasara.

 

“Za mu iya koyar da wannan a azuzuwa ga dalibanmu na jami’a. Idan za su iya zama a aji ba tare da fargabar yadda za su biya kudin makaranta ko abin da za su biya ba to za mu iya gina kasa mai nasara da wadata” in ji shi.

 

“Ina godiya ga Shugaban NRS da dukkan mutanen da ke cikin tawagar kula da harkokin tattalin arziki bisa irin ayyukan da muke gudanarwa. Ina ba ku tabbacin cewa ba zan daina karatu, tunani da kuma ba ku goyon baya ba” in ji shi.

 

Shugaban ya bayyana cewa bangaren masu zaman kansu yana da babban rawar da zai taka wajen bunkasa tattalin arziki ta hanyar samar da ayyukan yi da kuma tallafawa gwamnati.

 

“Idan muka karfafa gwiwar bangaren masu zaman kansu wajen zuba jari a fannin tattalin arziki cikin hikima to za mu samu ci gaba. Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa na goyi bayan Aliko Dangote tun kafin ma na zama Shugaban kasa. Allah ya yi wa Muhammadu Buhari rahama. Mun tattauna kan yadda za mu tallafa wa bangaren masu zaman kansu domin su shiga harkar tace man fetur”

 

Shugaban kasa ya jaddada cewa manufar cimma tattalin arziki mai darajar dala tiriliyan daya abu ne mai yiwuwa idan aka yi la’akari da yawan al’ummar kasar da kuma hazaka da karfin gwiwar mutanenta.

 

Ya bayyana cewa za a yi wa kamfanin NNPC garambawul tare da sanya shi cikin jerin kamfanonin da ake cinikin hannunjarinsu a kasuwar jari.

 

Ministan Kudi ya ce “Kasuwar hannunjari ta samu gagarumin ci gaba a ‘yan shekarun nan musamman a shekaru ukun da suka gabata sakamakon gyare-gyaren da aka yi a fannin tattalin arziki. Har ta kai ga cewa kasuwar jari ta Najeriya ita ce ta fi kowacce a duniya nuna kwazo. Kasuwar jari na daya daga cikin hanyoyin da suka fi saurin samar da arziki ga miliyoyin ‘yan Najeriya.

 

“Tare da Hukumar Kula da Kasuwar Jari (SEC) da sauran masu tsara dokokin fannin mun ga wadannan ci gaban, kuma mun san cewa suna aiki kan sabbin dabaru daban-daban musamman yadda za a jawo hankalin matasa su shiga kasuwar.

 

“Misali yawancin matasanmu suna saka kudinsu a kadarorin da ba na zahiri ba (kamar kudaden yanar gizo ko ‘cryptocurrency’) da kuma caca, alhali kuwa za su iya samun karin kudi ta hanyar kasuwar jari” in ji ministan.

 

Cardoso ya bayyana cewa sauyin da aka samu wajen karfafa jarin bankuna ya nuna akwai kwarin gwiwa kan tsarin harkokin kudi.

 

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce kwanciyar hankalin tattalin arziki zai jawo karin zuba jari kuma masu zuba jarin za su haifar da ci gaban da zai shafi bangaren samar da kayayyaki da ayyuka na tattalin arziki.

 

 

LADAN NASIDI

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button