Nishadi.

Najeriya Ta Nuna Goyon Bayanta Ga Karibi-George A Gasar Kyau Ta Duniya Ta Miss World

Najeriya ta bayar da cikakken goyon bayanta ga Queen Tamunosoye Karibi-George, wacce ke wakiltar kasar a gasar sarauniyar kyau ta duniya (Miss World) ta shekarar 2026 da za a gudanar a kasar Vietnam.

Yayin jawabi a wani babban taron gabatarwa da yi mata bankwana na kasa a Abuja, wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ‘yan majalisa, abokan huldar ci gaba, jakadun kasashen waje da masu shirya gasar, Ministar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma, Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim, ta bayyana shigar Karibi-George gasar a matsayin wani muhimmin mataki na diflomasiyyar al’adu, jagorancin mata, da kuma daukaka martabar kasa a idon duniya.

“Za ta daga tutarmu a daya daga cikin manyan dandamali da suka fi daukar hankali a duniya. Kuma za ta daga ta cikin nuna kwarjini, basira, da kuma alfahari,” in ji Ministar.

Ta hanyar bayyana gasar Miss World a matsayin dandamali na tasiri maimakon gasar kyau kawai, ta ce, “Wannan misali ne na diflomasiyyar al’adu a matakinta mafi inganci,” inda ta jaddada cewa shigar Najeriya gasar zai bayyana al’adun kasar, tattalin arzikin da ya dogara da kirkire-kirkire, da kuma karfin da mata ‘yan Najeriya ke da shi

Yayin da ta lura cewa wakiliyar za ta wakilci fiye da kanta kawai a fagen duniya, ta bai wa ‘yan Najeriya tabbacin goyon bayan gwamnati, inda ta ce, “Wannan ma’aikata tana ba da cikakken goyon baya na hukumance domin tabbatar da cewa shigarta gasar ya tafi cikin sauki, mutunci, da nasara… ba za a bar ta ta dauki wannan nauyin ita kadai ba.”

Da take kira ga hadin kan kasa, Ministar ta bukaci ‘yan kasa su “ba ta goyon baya… su yi mata addu’a… su karfafa mata gwiwa da murya daya,” tare da kara da cewa ko mene ne sakamakon gasar, “tuni ta cimma wani abu mai matukar muhimmanci.
Ta samu damar bayar da labarin Najeriya ga duniya.”

Babban Sakataren Ma’aikatar, Mrs. Nko Esuabana, ya yi tsokaci kan yadda gasar kyau ta wakilcin Najeriya ta samo asali da kuma yadda ta ci gaba, tare da bayyana kwarin gwiwar cewa za a sake samun nasarar da aka taba samu a baya.

“Za mu shiga gasar ta duniya ne domin dawowa da kambin nasara. An taba samun hakan a baya kuma za a sake samunsa, har sau da dama,” in ji ta.

Daraktan Kamfanin Silverbird Group—wanda shi ne ke shirya yadda Najeriya ke shiga gasar Miss World—Guy Murray-Bruce, ya bayyana Karibi-George a matsayin jakadiya ta musamman mai kwazo.

“Ta karɓi nauyin sarautar nan cikin natsuwa, tawali’u da kuma kudirin cimma manufa,” in ji shi, yayin da yake nuni da cewa gasar Miss World tana bayar da muhimmanci ga “kudirin cimma manufa, jagoranci, basira, hidima, ladabi da kuma ikon haifar da sauyi mai kyau.”

Ya jaddada cewa, “Muna da cikakken tabbacin cewa za ta wakilci ƙasar nan cikin mutunci, natsuwa da kuma kwarewa ta kololuwa.”

Da take mayar da martani, Sarauniya Tamunosoye Karibi-George, wadda ta nuna tsananin farin ciki da motsin rai, ta bayyana wannan lokaci a matsayin cikar burin rayuwarta.

“Hakika ina rayuwa a cikin wannan buri nawa,” in ji ta.

Ta yi alkawarin nuna kyawawan halayen Najeriya, inda ta ce, “Abu ne mai matukar muhimmanci a gare ni in wakilci ainihin halayenmu… tausayinmu, juriyarmu da kuma karfinmu a matsayinmu na al’umma.”

Yayin da take bayyana kwarin gwiwarta gabanin gasar karshe da za a yi a ranar 5 ga Satumba, 2026, ta ce, “Babban burina shi ne abin da ya faru shekaru 25 da suka gabata ya sake faruwa a ranar 5 ga Satumba,” sannan ta tabbatar wa magoya bayanta cewa, “Tabbas zan sa ku ji alfahari da ni.”

Shugabar Kwamitin Mata na Majalisar Wakilai, Kafilat Ogbara, ta tunatar da sarauniyar game da muhimmancin aikin da ke gabanta.

“Bari duniya ta ga cewa Najeriya kasa ce mai albarkar hazaka, kyawawan halaye, kirkire-kirkire, da kuma ruhin neman koli ba tare da gajiyawa ba. Ke ta fi sarauniyar kyau kawai; kina dauke da karfin dukkan matan Najeriya da matasan Najeriya,” in ji ta, inda ta kara da cewa “samun kambin yana da muhimmanci wajen zaburar da bil’adama. Amma gina gadoji na hadin kai tsakanin kasashe da barin tarihin ayyukan alheri da hidima ga al’umma, su ne manyan nasarori na gaske.”

A madadin Manajan Darakta kuma Shugaba na Hukumar Raya Yankin Niger Delta (NDDC), Samuel Ogbuku, Mrs. Kunemofa Asu Ekiye ta bukaci sarauniyar da ta tuna cewa “ba kambi kawai kike dauke da shi ba, kina dauke da nauyin aiki. Ki zama muryar bege, abin koyi na gaskiya da rikon amana, da kuma jakadiyar koli da nagarta.”

Darakta-Janar na Hukumar Kula da Kasuwar Hannun Jari (SEC), Dr. Imomotimi Agama, ya ce, “Ba wai kawai tana dauke da takardar da ke nuna matsayinta ba ne, tana dauke da bayanan da ke nuna darajar kasa… Tana dauke da martabar Najeriya,” inda ya kara da cewa “duk lokacin da dan Najeriya ya fito a dandalin duniya kuma ya nuna kansa cikin koli da nagarta, darajar kasarmu tana karuwa.”

An shirya wannan babban taron ne tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci Gaban Jama’a ta Tarayya, da kungiyar Miss World Nigeria, da Sarauniya Soye Karibi George, tare da goyon bayan wasu abokan hulda

 

 

Aisha.Yahaya,  Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button