Shugaba Tinubu Ya Isa Saudiyya Domin Gudanar Da Aikin Umrah

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Jeddah na kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah inda zai yi addu’o’in neman zaman lafiya hadin kai kwanciyar hankali da ci gaba mai dorewa ga kasar Najeriya.
Shugaban ya sauka a Filin Jiragen Sama na Kasa da Kasa na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah a ranar Alhamis inda Jakadan Najeriya a kasar Saudiyya Yakubu Gambo da Shugaban Sashen Kula da Harkokin Fadar Sarautar Saudiyya Ahmad bin Thafir suka tarbe shi.
Isar Shugaba Tinubu ta biyo bayan tashi daga Abuja ne a farkon ranar Alhamis wanda hakan ke nuni da fara ziyarar addini da ya kai kasar Saudiyya.
Shugaban ya tashi daga bangaren fadar shugaban kasa na Filin Jiragen Sama na Kasa da Kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 2:20 na rana inda gwamnonin jihohi da manyan jami’an gwamnati suka raka shi har filin jirgin.
Kafin tafiyarsa, Shugaba Tinubu ya kaddamar da sabbin helikopta guda biyar da Rundunar Sojan Sama ta Najeriya ta samu wadanda suka hada da helikopta guda biyu kirar Airbus H-125 da kuma guda uku kirar Agusta 109 Trekker B domin karfafa karfin aikin sojoji wajen yaki da ta’addanci da sauran barazanar tsaro.

Haka kuma ya kaddamar da sabon ginin ajiye jiragen sama na fadar shugaban kasa Hangar a filin jirgin.
Bayo Onanuga Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru ya sanar da tafiyar a ranar Laraba inda ya bayyana cewa ziyarar za ta ba da damar yin tunani na ruhaniya ibada da kuma yin addu’o’i domin kasar.
Kafin barin Abuja Jakadan Saudiyya a Najeriya Yousef Bin Mohammed Al-Balawi ya bai wa Shugaba Tinubu kyautar ‘Bisht’ wato doguwar rigar gargajiya ta Saudiyya a madadin Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron bankwana da shugaban akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume da gwamnoni da dama wadanda suka hada da AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara Babagana Zulum na jihar Borno Mai Mala Buni na jihar Yobe Uba Sani na jihar Kaduna Umar Namadi na jihar Jigawa da kuma Ahmad Aliyu na jihar Sokoto.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya a mako mai zuwa bayan kammala aikin Umrah din



