Masar Ta Kama Wasu Mutane Da Ake Zargi Da Hannu A Wani Shirin Zamba Ta Hanyar Yin Karya A Matsayin Alkalai.

Hukumomin Masar sun kama mutane da dama dangane da wani shiri na zamba da ya shafi mutanen da suka yi ikirarin cewa su alkalai ne, inda ake zarginsu da damfarar jama’a kudinsu.
Ma’aikatar Cikin Gida ta bayyana cewa, ana zargin wadanda ake tuhumar da shirya zaman kotu na bogi da kuma yin amfani da sunan alkali a shafukan sada zumunta domin yaudarar mutane su ba su kudi.
A cewar ma’aikatar, an tsare manyan wadanda ake zargin—wani mutum da ba shi da aiki da kuma wani dalibi mazauna biranen Alkahira da Giza—yayin da ake ci gaba da bincike domin gano da kuma kama sauran mambobin kungiyar masu zambar.
KARANTA KUMA: Najeriya za ta kara da Masar a wasa mai muhimmanci na gasar WAFCON
Ma’aikatar ta kara da cewa, bayan an yi musu tambayoyi, sun amsa laifin kafa kungiyar masu aikata laifi da ke karbar kudi daga hannun ‘yan kasa ta hanyar yin ikirarin karya cewa za su iya samar musu da gidaje daga hukumomin gwamnati.
Haka kuma, an ce sun amsa laifin shirya zaman kotu na bogi tare da taimakon wasu mutane.
Jaridar gwamnati ta *al-Ahram* ta bayyana cewa an tsare mutane da dama da ake zargin sun shiga cikin shirin zambar, kuma an tura su domin fuskantar shari’a cikin gaggawa.
An ce an gano shirin ne bayan hukumomi sun fara bincike sakamakon ikirarin da wani mutum ya yi cewa wani ya yi masa zamba ta hanyar gabatar da kansa a matsayin alkali.
Jaridar ta ce an kama babban wanda ake zargin, inda ‘yan sanda suka kwace bindiga, da kayan aikin alkali (kamar bel din da alkalai ke sawa), da kuma katunan shaida dauke da mukamin alkali na bogi.
An kuma ce ya amsa laifin daukar hotuna da bidiyo a cikin zauren kotu yayin da yake sanye da kayan aikin alkali domin ya sa mutane su amince da shi.
Jaridar ta ruwaito cewa ya amsa cewa wani mutum na biyu ya taimaka masa, tare da taimakon wasu ma’aikatan kotu.
A cewar masu gabatar da kara, an ce mutum na biyu da ake zargi ya amsa laifin shiga cikin aikin daukar hoto da bidiyo da kuma wallafa su, yayin da yake ikirarin cewa shi alkali ne a shafukan sada zumunta.
Jaridar ta kara da cewa an kuma tsare ma’aikatan kotun tare da yi musu tambayoyi, inda suka yi ikirarin cewa babban wanda ake zargin ya gaya musu cewa yana aiki ne da daya daga cikin hukumomin shari’a na Masar.
BBC/Aisha.Yahaya, Lagos



