Fitattun LabaraiNajeriya

INEC za ta gudanar da gwajin tantance masu kada kuri’a a fadin kasar nan gabanin zaben 2027

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Joash Amupitan ya bayyana cewa an tsara gudanar da gwajin tantance masu zabe a fadin kasar baki daya a watan Nuwamban 2026 domin auna shirin hukumar gabanin Babban Zaben 2027.

 

Wannan na zuwa ne yayin da ya bayyana yadda hukumar ta gudanar da zaben gwamnan Jihar Osun a matsayin abin koyi na kololuwar inganci wajen tafiyar da harkokin zabe.

 

Shugaban na INEC ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a 21 ga watan Agusta 2026 a Abuja yayin da yake karbar bakuncin Mukaddashin Jakadan Kanada a Najeriya Mista David Sproule da Wakilin kungiyar Konrad Adenauer Stiftung (KAS) a kasar Mista Moritz Sprenker wadanda suka kai ziyarar ban girma a hedikwatar hukumar.

 

KARANTA KUMA: NITP ta yi kira da a samar da ka’idojin tsara birane a fadin kasar

 

Farfesa Amupitan ya ce zaben Jihar Osun wanda aka gudanar a ranar Asabar 15 ga watan Agusta 2026 ya nuna sakamakon hangen nesa a fannin gudanarwa da kuma ingancin fasaha inda ya bayyana cewa cibiyoyin zabe 3,556 cikin 3,763 da ke jihar wato kashi 94.5 na jimillar cibiyoyin sun bude domin fara tantance masu zabe da kada kuri’a da misalin karfe 8:30 na safe.

Ya danganta wannan sakamako da ingantaccen aikin na’urar tantance masu kada kuri’a ta BVAS a wuraren zabe da kuma yadda aka tura sakamakon zaben zuwa shafin yanar gizo na INEC (IReV) ba tare da matsala ba tare da yadda jami’an zabe suka tunkari matsaloli cikin hikima da gaggawa.

 

“Ba mu dauki nasarar da aka samu a jihar Osun a matsayin karshen tafiya ba, sai dai a matsayin misali mai inganci da zai jagoranci shirye-shiryenmu na zaben shekarar 2027” in ji Shugaban Hukumar.

 

Baya ga nasarar da aka samu a Osun Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumar za ta gudanar da gwajin tantance masu kada kuri’a a watan Nuwamba na shekarar 2026 a matsayin wani bangare na shirye-shiryen babban zaben kasa ya bayyana hakan a matsayin muhimmin gwaji na zahiri ga na’urar BVAS domin tabbatar da amincin tsarin zabe kafin babban zaben 2027.

 

Ya nuna godiyarsa ga kasar Canada bisa ci gaba da hadin gwiwar da take bayarwa wajen tabbatar da nasarar wannan shiri.

 

Farfesa Amupitan ya kuma yi magana kan bukatar sake tantance bayanan masu kada kuri’ainda ya bayyana cewa akwai bukatar a sake tabbatar da bayanan adadi mai yawa na masu kada kuri’a musamman tsofaffi wadanda suka yi rajista tun shekarar 2011.

 

Ya ce ya kamata a gudanar da wannan shiri kafin babban zaben 2027 domin kaucewa duk wani jinkiri a harkokin zabe na gaba.

 

Shugaban INEC ya lura cewa wadannan ayyuka biyu sun zo ne a wani muhimmin lokaci a jadawalin hukumar kasancewar an tsara gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokoki ta Kasa a ranar Asabar 16 ga watan Janairun 2027 yayin da aka tsara zaben Gwamnoni da na Majalisar Dokoki ta Jiha a ranar 6 ga watan Fabrairun 2027.

 

Ya tuna cewa ranar Laraba 19 ga watan Agustan 2026 ita ce ranar fara yakin neman zabe a bainar jama’a domin babban zaben 2027 kuma hukumar ta riga ta halarci taron da Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa ya shirya tare da ‘yan takarar shugaban kasa da shugabannin jam’iyyu inda aka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta farko ta kasa da ta mayar da hankali kan yakin neman zabe mai dogaro da batutuwan da suka shafi ci gaban kasa.

 

Ladan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button