Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Yi Maraba Da Ceto mutane 308 Da Aka Sace.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi maraba da nasarar ceto ‘yan kasa 308 da aka sace, a cikin ayyukan tsaro da aka gudanar tare da hadin gwiwa a jihohin Neja da Kwara; inda ya yaba wa Rundunar Soji da sauran hukumomin tsaro bisa gudanar da babban aikin ceto na rana daya mafi girma a tarihin hadin gwiwar jami’an tsaro.

Shugaban ya bayyana cewa, mutane 163 daga cikin wadanda aka ceto din an sace su ne daga yankin Woro da ke Karamar Hukumar Kaiama a Jihar Kwara, yayin da sauran mutane 145 aka ceto su ne a Jihar Neja.

Wata sanarwa da mai bai wa Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa, an ceto wadanda abin ya shafa ne daga dajin  shakatawa na kasa na Kainji Lake (Kainji Lake National Park) da ke Karamar Hukumar New Bussa a Jihar Neja, bayan wani aiki da aka gudanar bisa bayanan sirri karkashin jagorancin Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa (NCTC), tare da hadin gwiwar jami’an Rundunar Sojin Najeriya, da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da kuma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

Shugaba Tinubu ya yaba wa shugabannin da ma’aikatan hukumomin tsaro saboda jarumtakarsu, hadin gwiwa da jajircewarsu, yana mai cewa nasarar aikin yana nuna yadda tsarin tsaron Najeriya ke bunkasa.

“Nasarar aiwatar da wannan aikin da jami’an leken asiri suka jagoranta ya nuna karuwar inganci da hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaronmu.

Ina yaba wa jaruman maza da mata masu sanye da kayan soja saboda jarumtakarsu da jajircewarsu wajen kare rayukan ‘yan Najeriya,” in ji Shugaban.

Bayan kammala tantance lafiyarsu, sanarwar ta kara da cewa za a mika su ga gwamnatocin jihohinsu domin samun cikakken kulawa da sake hadewa da iyalansu.

Yayin murnar dawowar wadanda abin ya shafa lafiya, Shugaba Tinubu ya umurci hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki da su karfafa tsarin gargadin gaggawa, inganta tattara bayanan sirri na al’umma da kuma inganta karfin mayar da martani cikin sauri don hana irin wadannan hare-hare a fadin kasar.

Shugaban ya kuma sake jaddada kudirin gwamnatinsa na magance rashin tsaro, yana mai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnati ta dage wajen kawar da barazanar tsaro, kare al’ummomi masu rauni da kuma dawo da zaman lafiya mai dorewa a duk fadin kasar.

 

 

Aisha.Yahaya,  Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button