Afirka

Ministan Harkokin Wajen Jamus Ya Ziyarci Najeriya Domin Tattaunawa Da Bangarorin Biyu.

Ministan Harkokin Wajen Jamus, Mista Johann Wadephul, zai ziyarci Najeriya daga ranar 21 zuwa 22 ga watan Yuli domin gudanar da tattaunawa ta manyan jami’ai tare da wakilan gwamnatin Najeriya, da nufin karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, fadada harkokin kasuwanci da zuba jari, da kuma inganta hadin gwiwa a yankin.

Shugaban sashen yada labarai kuma mai ba da shawara kan harkokin siyasa a ofishin jakadancin Jamus, Mista Felix Haala, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Juma’a a da ta gabata a Abuja.

Haala ya ce Wadephul zai ziyarci Abuja da Legas, tare da tawagar ‘yan kasuwa da suka hada da shugabanni da manyan jami’ai daga manyan kamfanonin Jamus a fannonin fasahar sadarwa (IT) da makamashi, da kuma ‘yan majalisar dokokin Jamus.

A cewarsa, ministan zai gudanar da tattaunawa a Abuja tare da Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Madam Bianca Odumegwu-Ujukwu, da Shugaban Hukumar Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Dr. Omar Touray.

KARANTA KUMA: Najeriya da Jamus sun karfafa hadin gwiwa kan manufofin samar da gidaje

Ya ce tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi ci gaban yankin, zaman lafiya da tsaro, hadewar tattalin arziki, da kuma damar karfafa hadin gwiwa tsakanin Jamus da Yammacin Afirka.

Haala ya kara da cewa, bangaren ziyarar a Legas zai mayar da hankali ne kan inganta dangantakar tattalin arziki da al’adu, inda aka tsara Wadephul zai halarci taron tattaunawa na ‘yan kasuwa da ya kunshi kamfanonin Jamus da na Najeriya.

Ya ce taron zai bayyana karuwar hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu tare da binciko sabbin damammaki na kasuwanci da zuba jari.

A cewar Haala, Jamus da Najeriya na da kyakkyawar dangantaka mai karfi da ta ginu kan mutunta juna da kuma moriyar juna, inda Najeriya ta kasance daya daga cikin muhimman abokan hulda na Jamus a Afirka.

Ya bayyana cewa ziyarar na nuna kudurin Jamus na zurfafa hadin gwiwa da Najeriya da kuma yankin Yammacin Afirka baki daya a fannoni da suka hada da ci gaban tattalin arziki mai dorewa, sauye-sauye a fannin makamashi, da kuma zaman lafiya da tsaron yankin.

 

 

NAN/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button