Mutanen Da Suka Dawo Gida Sun Yaba Wa Shugaba Tinubu Kan Fitar Da Su Daga Afirka Ta Kudu.

Kusan ‘yan Najeriya 1,500 da aka kwaso daga Afirka ta Kudu bayan hare-haren nuna kyama ga baki (xenophobia) sun yaba wa Shugaba Bola Tinubu bisa daukar nauyin dawowarsu da kuma taimaka musu wajen sake gina rayuwarsu.
Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) ta kuma yi kira ga karin gwamnatocin jihohi, kungiyoyi masu zaman kansu, da kuma ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su tallafa wa wadannan mutane yayin da suke kokarin sake farfado da rayuwarsu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na NiDCOM, Abdur-Rahman Balogun, ya fitar, Shugabar hukumar, Dr. Abike Dabiri-Erewa, ta nuna godiyarta ga Shugaba Tinubu bisa daukar nauyin dukkan tsarin kwaso mutanen.
KARANTA KUMA: Najeriya ta sake jaddada kudirinta na taimaka wa wadanda suka dawo su sake shiga cikin al’umma
“Muna matukar godiya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa daukar nauyin kwaso ‘yan kasarmu da kuma taimaka musu wajen sake gina rayuwarsu. Wannan mataki ya nuna irin kudirin gwamnati na kula da jin dadin ‘yan Najeriya a duk inda suke,” in ji ta.
Tallafin Jihohi Da Kungiyoyi
Dabiri-Erewa ta yaba wa gwamnatocin jihohi, kamfanoni, kungiyoyin addini, da masu hannu da shuni wadanda suka bayar da tallafin kudi, masauki, shirye-shiryen samar da sana’o’i, da sauran nau’o’in tallafi.
Ta bayyana gudummawar da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, da Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, suka bayar, inda kowannensu ya yi alkawarin bayar da Naira miliyan 1 ga ‘yan jihohinsu da lamarin ya shafa
A cewarta, jihohin Delta, Anambra, Abia, Enugu, da Lagos suma sun tallafa wa ‘yan jihohinsu da suka dawo, yayin da ta yi kira ga sauran jihohi su bayar da irin wannan tallafin.
Yabon Kungiyoyin Tallafi
Shugabar NiDCOM ta yaba da tallafin da Apostle Chibuzor Gift Chinyere na kungiyar Omega Power Ministries (OPM) ya bayar, inda ya samar da masauki ga iyalai 57 da suka dawo, tare da samar musu damar koyon sana’o’i da ilimi kyauta ga ‘ya’yansu.
Ta kuma yaba wa kamfanin MTN Nigeria bisa bai wa kowane mutum da ya dawo fakitin SIM mai dauke da ‘data’ ta darajar Naira 50,000 da kuma tallafin kudi na Naira 100,000.
Sauran masu bayar da tallafi sun hada da gidauniyar JAAL Foundation, wacce ta karfafa gwiwar mata 50 da suka dawo gida; Cocin Harvesters, wanda ya bai wa mutane 66 da suka dawo tallafin Naira 100,000 ga kowannensu; kamfanin Cruxstone Real Estate; da kuma gidauniyar Oyakhilome Foundation, wacce ta raba kayan abinci ga wadanda suka dawo.
“Muna matukar godiya ga karamcin gwamnatocin jihohinmu, kamfanoni, kungiyoyin addini da kuma daidaikun mutane da suka nuna tausayi ta hanyar tallafawa wadanda suka dawo,” in ji Dabiri-Erewa.
Kira Ga Karin Tallafi
Yayin da take yabon hukumomi irin su NEMA, FAAN, NIMC, Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Masu Hijira da kuma Wadanda Rikici ya raba da muhallansu (NCFRMI) bisa saukaka tsarin dawowar, Dabiri-Erewa ta yi kira ga karin gwamnoni, ‘yan kasuwa da kuma ‘yan Najeriya masu kyakkyawar niyya da su tallafa wa wadanda suka dawo.
“Wannan nauyi ne na kasa baki daya, kuma tare za mu iya taimaka musu wajen sake shiga cikin al’umma cikin nasara,” in ji ta.
Shirin kwaso mutane bisa radin kai, wanda aka gudanar daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yuli, ya dawo da ‘yan Najeriya 1,490 da suka makale a Afirka ta Kudu zuwa gida ta hanyar jiragen sama guda biyar na kamfanin Air Peace, wadanda Gwamnatin Tarayya ta dauki nauyinsu bisa umarnin Shugaba Tinubu.
Aisha.Yahaya, Lagos



