
Ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Arewacin Najeriya Arewa for Asiwaju (A4A) ta bayyana aniyarta ta haɗa gwiwa da ƙungiyar Tinubu Mass Mobilization Network (TMMN) domin wayar da kan al’umma da ƙarfafa goyon baya ga Shugaba Tinubu gabanin zaɓen shekarar 2027.
A4A ta tabbatar da hakan ne yayin da Darakta-Janar ɗinta tsohon Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya karɓi baƙuncin shugabannin ƙungiyar TMMN a hedikwatar A4A da ke Abuja.
Da yake jawabi Shugaban TMMN Honarabul Zaharadden Zakari ya bayyana cewa ƙungiyar tana da mambobi sama da dubu ashirin a faɗin jihohin Arewacin Najeriya 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ya ce tuni ƙungiyar ta fara gudanar da ayyukanta a matakai daban-daban inda take shiga lungu da saƙo domin tattara magoya baya tare da wayar musu da kai kan zaɓen 2027 da ke ƙara gabatowa.
Dangane da korafe-korafen da wasu ‘yan Najeriya ke yi kan cire tallafin man fetur Honarabul Zaharadden ya bayyana cewa akwai buƙatar al’umma su fahimci cewa matsalar tashin farashin makamashi ba ta Najeriya kaɗai ba ce illa matsala ce da ta shafi ƙasashe da dama a duniya.
A nasa jawabin Darakta-Janar na A4A Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya tabbatar wa tawagar TMMN cewa ƙungiyarsa a shirye take ta yi aiki tare da su domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai da haɗa ƙarfi wajen wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da nasarar manufofin ƙungiyoyin biyu.
Tun da farko ƙungiyar TMMN ta sha alwashin kai ziyarar wayar da kai zuwa ƙananan hukumomi 413 da ke Arewacin Najeriya domin ilmantar da al’umma kan shirye-shirye da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daga cikin ayyukan da ƙungiyar ta ce za ta riƙa bayyana wa al’umma akwai bunƙasa harkokin sufurin jiragen ƙasa matakan rage tsadar kayan abinci samar da ma’aikata da tsare-tsare domin bunƙasa kiwon dabbobi da sauran shirye-shiryen da gwamnatin ke ganin za su taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Musa Aminu



