Duniya

Amurka Ta Rasa Matsayinta Na Kasa Marar Cutar Kyanda Bayan Shekaru 26

Hukumar Lafiya ta Pan American Health (PAHO) ta soke matsayin kawar da kyanda a Amurka bayan ta tabbatar da cewa kasar ta gaza dakatar da ci gaba da yada kwayar cutar mai saurin yaduwa fiye da shekara guda.

Wannan hukunci ya kawo karshen tarihin Amurka na shekaru 26 na rashin kamuwa da cutar kyanda mai dorewa yayin da bayanai suka nuna mafi girman adadin wadanda suka kamu da cutar kyanda a cikin shekaru sama da talatin.

Kimanin mutane 7,500 ne suka kamu da cutar a kasar tun daga shekarar 2025 inda aka samu mutuwar mutane 13.

PAHO ta sake duba shaidun cututtuka da dakin gwaje-gwaje da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka ta gabatar don tantance ko irin wannan kwayar cutar kyanda ta yadu a Amurka ba tare da katsewa ba tsawon watanni 12 ko fiye wata alama ce ta yaduwar cutar a gida maimakon wadanda aka shigo da su daga waje.

KARANTA KUMA: Amurka Ta Tabbatar Da Mutuwa Shida Masu Alaƙa Da Cutar Kyanda A 2026

Dr Erica Schwartz darektan Cibiyar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Amurka ta ce idan Amurka ta rasa kawar da cutar kyanda hukumar za ta yi “Irin wannan abu” wanda ya kunshi yin aiki tare da jihohi don karfafa rigakafi.

An bayar da rahoton mutane 5,182 da aka tabbatar sun kamu da cutar kyanda a shekarar 2026 ga Cibiyoyin Kula da Cututtuka da Rigakafi na Amurka daga jihohi 45 Birnin New York da Gundumar Columbia wanda ya zarce jimillar mutane 2,289 na bara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button