Kasuwanci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudirin Kafa Jami’ar Yusuf Maitama Sule.

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar kafa tsarin gudanarwa na doka ga Jami’ar Ilimi ta Tarayya mai suna Yusuf Maitama Sule da ke Jihar Kano matakin da zai ba da damar gudanar da harkokinta da kuma ci gabanta a hukumance.

An amince da kudirin—wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin mai wakiltar Kano ta Arewa ya gabatar—a yayin zaman majalisar da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya jagoranta.

Wata sanarwa daga Ismail Mudashir Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta bayyana cewa kudirin na da nufin samar da tushen doka don gudanar da makarantar tare da karfafa fannin horar da malamai a Najeriya.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa na Matsin Lambar Yin Gyare-gyare don Kare Bangaren Man Fetur na Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya amince da sauya Kwalejojin Ilimi na Tarayya da ke Kano da Zaria zuwa Jami’o’in Ilimi na Tarayya a watan Satumbar 2024.

Daga baya an sanya wa makarantar da ke Kano sunan marigayi fitaccen dan siyasar Najeriya Yusuf Maitama Sule biyo bayan amincewar shugaban kasa a ranar 10 ga watan Mayun 2025.

Barau ya bayyana cewa kudirin zai taimaka wajen ingantawa da bunkasa fannin horar da malamai yayin da Akpabio ya yaba masa bisa gabatar da kudirin tare da nuna kwarin gwiwar cewa Shugaba Tinubu zai sanya hannu a kansa da zarar an mika masa shi.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button