Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya Bayan Gudanar Da Aikin Hajji A Saudiyya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala aikin Umrah a Masarautar Saudiyya.
Shugaban ya isa Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 8:53 na dare a ranar Laraba 4 ga watan Nuwamba 2026.
Wadanda suka tarbi Shugaban sun hada da Shugaban Ma’aikatansa Femi Gbajabiamila Ministan Ilimi Dr. Olatunji Alausa Karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Olatunji Disu da sauran manyan jami’an gwamnati.
Dawowar Shugaba Tinubu ta biyo bayan ziyarar da ya kai birnin Makkah mai alfarma inda ya gudanar da aikin Umrah tare da yin addu’o’in neman zaman lafiya hadin kai kwanciyar hankali da ci gaba mai dorewa ga Najeriya.
KARANTA KUMA:http://Shugaba Tinubu ya bar Saudiyya ya nufi Abuja
A yayin gudanar da aikin ibadar Shugaban ya samu damar shiga cikin dakin Ka’aba mai alfarma wani gata na musamman da ke nuna zurfin dangantaka da hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Masarautar Saudiyya.

Shugaba Tinubu ya tashi daga sashen da aka tanada na musamman (Royal Terminal) a Filin Jirgin Sama na Kasa da Kasa na King Abdulaziz da ke Jeddah da misalin karfe 5:13 na yamma agogon Saudiyya.
KARANTA KUMA:http://A CIKIN KA’ABA: GATA NA MUSAMMAN DA SAKON DAGA MAKKAH
Kafin tafiyarsa Shugaba Tinubu ya yi wani gajeren taro da Mataimakin Gwamnan yankin Makkah Yarima Saud bin Mishaal bin Abdulaziz Al Saud a fadar baki ta musamman da ke cikin filin jirgin saman.
Mataimakin Gwamnan tare da Jakadan Najeriya a Saudiyya Yakubu Gambo da Karamin Jakada (Consul-General) Muazam Ibrahim Nayaya sun raka Shugaban zuwa filin jirgin saman.

Aikin ibadar ya bai wa Shugaba Tinubu damar yin tunani na ruhaniya nuna godiya da kuma sabunta kudirinsa na gina Najeriya mai zaman lafiya hadin kai da wadata.
Shugaban ya kuma nuna godiyarsa ga Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud da Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman bisa karbar baki da kuma girmamawa ta musamman da suka nuna masa da tawagarsa. Tawagar shugaban ƙasar ta haɗa da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa Malam Nuhu Ribadu da gwamnonin jihohin Sakkwato Jigawa Kaduna Borno da Yobe da sauransu.



