Najeriya

Jakadan Najeriya A Isra’ila Ta Gabatar Da Takardun Shaidar Aikin Jakadanci

Jakadiyar Najeriya ta musamman kuma mai cikakken iko a kasar Isra’ila Jakadiya Nkechi Linda Ufochukwu ta fara gudanar da ayyukanta na diflomasiyya a hukumance bayan ta gabatar da takardun shaidar aikinta ga Shugaban kasar Isra’ila Isaac Herzog.

 

Ta gabatar da takardun ne a wani biki na musamman da aka gudanar a birnin Kudus (Jerusalem).

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Kimiebi Ebienfa ya bayyana cewa gabatar da takardun na nuni da fara aikin Jakadiya Ufochukwu a matsayin wakiliyar Najeriya a Isra’ila a hukumance tare da jaddada kudirin gwamnatin Najeriya na karfafa dangantakar diflomasiyya mai dorewa tsakanin kasashen biyu.

 

Da take jawabi bayan kammala bikin Jakadiya Ufochukwu ta bayyana aniyarta ta zurfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Isra’ila a lokacin da take kan mukamin.

 

Ta sake jaddada kudirinta na “ci gaba da aiwatar da manufofin harkokin wajen Najeriya tare da inganta hadin gwiwa a fannonin da kasashen biyu ke da moriyar juna a kansu.”

 

KARANTA KUMA: Najeriya na karfafa dangantaka da kasar Switzerland

 

A cewar jakadiyar “aikinta zai mayar da hankali sosai kan fadada hadin gwiwa a fannonin kasuwanci da zuba jari da noma da fasaha da tsaro da kirkire-kirkire da musayar al’adu tare da karfafa alaka tsakanin al’ummar kasashen biyu domin amfanin juna.”

 

Ma’aikatar harkokin waje ta bayyana kwarin gwiwar cewa nadin Jakadiya Ufochukwu zai kara karfafa dangantaka mai muhimmanci tsakanin Najeriya da Isra’ila.

 

Ta kuma yi nuni da cewa ana sa ran aikin diflomasiyyarta zai samar da sabbin damammaki don inganta hadin gwiwa bunkasar tattalin arziki da ci gaba mai dorewa.

 

Gabatar da takardun shaidar aikin na nuni da ci gaba da kudirin Najeriya na karfafa dangantakar diflomasiyya da Isra’ila da kuma inganta hadin gwiwa a muhimman fannoni da za su amfani kasashen biyu.

 

 

 

LADAN NASIDI

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button