Minista Ya Dora Wa Kungiyar APC Alhakin Hada Kan Jama’a a Matakin Tushe

An bukaci mambobin kungiyar tallafawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai suna ‘Project Beyond’ da su kara kaimi wajen hada kan jama’a a matakin tushe domin samun kuri’u ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Cross River Bassey Otu da sauran ‘yan takarar jam’iyyar a babban zaben shekarar 2027.
Ministan Jiha a Ma’aikatar Masana’antu ta Najeriya Sanata John Owan-Enoh ne ya bayar da wannan umarni a birnin Calabar babban birnin Jihar Cross River da ke yankin kudancin Najeriya yayin kaddamar da tsarin gudanarwar kungiyar ta ‘Project Beyond’ na yankin sanata na kudanci.
Owan-Enoh wanda ya jaddada cewa manufar ita ce samun nasara ga jam’iyyar APC a dukkan mazabu 196 na Jihar Cross River ya bukaci mambobin da su wuce matakin gudanar da bukukuwa kawai su kuma mayar da hankali kan samar da sakamakon zabe na zahiri ta hanyar tuntuɓar masu zabe kai tsaye a cikin al’ummominsu.
Ya ce “Ba ku zo nan sanye da hulunanku da rigunanku na jam’iyya don kawai yin biki ba ne. Kun zo nan ne domin a ba ku amana da jagorancin da za ku yi aiki da su don ku kawo mana sakamako mai gamsarwa.”
KARANTA KUMA: Gwamnan Cross River Ya Kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben na APC
Ministan ya kara da cewaqq kungiyar ‘Project Beyond’ ta kuduri aniyar sauya sakamakon babban zaben shekarar 2027 a Jihar Cross River ta hanyar tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta lashe dukkan kananan hukumomi 18 na jihar.
“Kudurin ‘Project Beyond Cross River’ tare da hadin gwiwar shugabannin jam’iyyar APC shi ne tabbatar da samun nasara a dukkan kananan hukumomi 18. Muna mai da hankali ne kan yawan kuri’un da za a samu,” in ji Owan-Enoh.
Ya bukaci masu gudanar da ayyukan (coordinators) da su koma mazabun zabe kasuwanni da al’ummomin da aka sanya su domin neman goyon baya ga ‘yan takarar jam’iyyar wadanda suka hada da shugaban kasa da gwamna da mataimakin gwamna da sanatoci da ‘yan majalisar wakilai ta tarayya da ta jiha.

“Ku buga kofofin gidaje. Ku je kasuwanni ku duba ko’ina kuma ku tabbatar kun sa mutane su fahimci dalilin da ya sa yake da muhimmanci su ba Shugaba Tinubu kuri’unsu domin ya ci gaba da zama Shugaban Tarayyar Najeriya,” in ji shi.
Owan-Enoh ya kuma yi kira ga mambobin da su hada kai wajen neman goyon bayan sake zaben Gwamna Otu da mataimakinsa, da kuma Sanata Asuquo Ekpenyong tare da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC da ke neman kujerun majalisa a jihar.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa masu gudanar da ayyukan za su samar da kuri’u masu yawa ga jam’iyyar inda ya jaddada cewa aikin yana bukatar ci gaba da tattaunawa da masu zabe ba wai kawai halartar tarukan siyasa ba.
Game da tsarin kungiyar tallafawa, ministan ya bayyana cewa asalin shirin shi ne kaddamar da dukkan tsarin kungiyar na jihar Cross River wanda ya kunshi mambobi kusan 20,000 a karamar hukumar Ikom.
Ya ce “Mun yi shirin kaddamar da kungiyar tallafawar a Ikom amma za mu bukaci motocin bas kusan 1,000 domin daukar mambobi 20,000 din. Saboda haka muka yanke shawara a lokacin karshe cewa za mu kaddamar da bangaren kudancin jihar a nan Calabar babban birnin jihar.”
Ya bayyana cewa an shirya wannan kaddamarwar ne kafin taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC wanda aka tsara gudanarwa a filin wasa na U.J. Esuene da ke Calabar inda ya nuna kwarin gwiwar cewa mambobin kungiyar za su fito da yawa.
Daya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a yayin kaddamarwar shi ne gudanar da aikin bayar da tallafin kiwon lafiya kyauta wanda matar Ministan Rachel Owan-Enoh ta dauki nauyinsa kuma ya amfani mazauna yankin da mambobin kungiyar.
Ayyukan da aka bayar sun hada da auna hawan jini gwajin zazzabin cizon sauro gwajin ido gwajin matakin sukari a jini bayar da magunguna kyauta tabarau da kuma tura marasa lafiya zuwa asibitoci domin samun kulawa ta musamman.
Aisha.Yahaya, Lagos



