Gasar Cin Kofin Duniya Ta FIFA U-17: Tawagar Flamingos Ta Tsallake Zuwa Matakin Kusa Da Na Karshe

Kungiyar ‘Flamingos’ ta Najeriya ta samu gurbi a matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 17 (FIFA U17 Women’s World Cup) bayan ta doke Venezuela da ci 1-0 inda Azeezatt Oduntan ta zura kwallo ta bugun fenariti a minti na 89 na wasan.
Wasan na matakin daf da na karshe ya kasance mai zafi da fafatawa sosai inda Najeriya ta samar da damammaki da dama amma ta ci karo da babban cikas daga mai tsaron ragar Venezuela Valeria Rebanales. ‘Flamingos’ sun fi mamaye bangaren kai hari a rabin lokaci na farko sai dai Rebanales ta yi nasarar ceto kwallaye da dama wanda hakan ya sa aka ci gaba da tashi babu ci.
An kuma bai wa dan wasan tsakiya Favour Nkwocha gargadi (katin gargadi) yayin da Najeriya ta ci gaba da matsa lamba domin samun kwallon farko.
Babban kocin kungiyar Hakeem Busari ya yi sauyin ‘yan wasa na farko a wasan inda ya shigo da Precious Oscar a madadin Oluwakemi Adegbuyi a yayin da Najeriya ke kokarin neman hanyar samun nasara.
KARANTA KUMA: Gasar Cin Kofin Duniya na Mata ‘Yan Kasa da Shekaru 17:
‘Flamingos’ Sun Doke Mexico Sun Tsallake Zuwa Matakin Da Fda Na Karshe
An ci gaba da rashin samun kwallo har zuwa minti na 88 lokacin da alkalin wasa ya bai wa Najeriya bugun fenariti kafin daga bisani ya duba na’urar VAR domin sake tantance hukuncin. Bayan an duba an tabbatar da bugun fenaritin inda Oduntan ta fito ta zura kwallon a raga yayin da ya rage minti daya kacal a tashi wasan wanda hakan ya bai wa Najeriya nasarar da take bukata.
Oluebube Umejiaku wacce ita ce kan gaba wajen zura kwallaye ce ta samar da damar bugun fenaritin ga kungiyar ‘Flamingos’ wanda ya bai wa Oduntan damar zama gwarzuwar da ta kawo sauyi a wasan.
Wannan nasarar ta kai Najeriya matakin kusa da na karshe inda za ta fafata da Brazil wacce ta doke China da ci 2-1 a wasanta na matakin daf da na karshe.
NFF/Aisha.Yahaya, Lagos



