Siyasa

Jam’iyyar APGA Ta Lashe Dukkan Kujerun Shugabancin Kananan Hukumomi

Safina Umar Farouk

Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta lashe dukkan kujerun shugabancin kananan hukumomi 21 da na kansiloli 346 a zaben kananan hukumomin jihar Anambra.

Shugabar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Anambra (ANSIEC) Chinel Osakwe ta sanar da sakamakon zaben a ranar Lahadi a hedikwatar hukumar da ke Awka babban birnin jihar.

Osakwe ta bayyana cewa an gudanar da zaben ne a dukkan kananan hukumomi 21 da mazabun zabe 362 na jihar bisa dokoki da ka’idojin zabe na jihar.

Ta ce a kananan hukumomi 20 babu wani dan takara daga wata jam’iyya da ya kalubalanci ‘yan takarar APGA inda aka gudanar da tsarin kada kuri’ar amincewa (“Yes”) ko rashin amincewa “No” ga ‘yan takarar APGA din.

Daga bisani hukumar ta ayyana ‘yan takarar APGA a matsayin wadanda suka yi nasara bayan sun samu kuri’un amincewa (“Yes”) masu yawa a yankunansu.

A zaben shugaban karamar hukuma daya tilo da aka yi takara tsakanin jam’iyyu daban-daban wato a karamar hukumar Anambra ta Gabas (Anambra East) Ifeanyi Chinweze na jam’iyyar APGA ya samu kuri’u 50,169 inda ya doke dan takarar jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) wanda ya samu kuri’u 1,658.

KARANTA KUMA: Mutanen da ke da nakasa za su shiga zaben Anambra

Osakwe ta ce hukumar ta yi nazari sosai kan sakamakon da jami’in tattara sakamakon zabe ya gabatar kafin ta ayyana dan takarar da ya samu mafi yawan ingantattun kuri’u a matsayin wanda ya yi nasara.

Ta bayyana yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali tare da jaddada cewa hukumar ta gudanar da ayyukanta cikin adalci gaskiya da kuma kwazo.

Shugabar ta ANSIEC ta yaba wa al’ummar Anambra bisa amincewarsu da hukumar tare da yaba wa hukumomin tsaro da kafofin yada labarai kan goyon bayan da suka bayar yayin gudanar da zaben.

Da yake magana a madadin sabbin shugabannin kananan hukumomin da aka zaba wanda aka zaba a matsayin shugaban karamar hukumar Ayamelum Emmanuel Igwebuike ya yaba wa Gwamna Chukwuma Charles Soludo hukumar ANSIEC hukumomin tsaro, da kafofin yada labarai bisa samar da yanayi mai kyau da ya ba da damar gudanar da zaben cikin nasara.

Igwebuike ya yi alkawarin cewa sabbin shugabannin kananan hukumomin za su goyi bayan tsarin ci gaban da gwamna ya shimfida da kuma hangen nesansa na mayar da Anambra jiha mai kyau da wadata nan da shekarar 2070.

 

 

Safina Umar Farouk.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button