Afirka

Shugaban Sudan Ta Kudu Ya Cire Gwamnan Babban Bankin Kasar.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit> ya kori Gwamnan babban bankin kasar, Johnny Ohisa, a wani sabon zagaye na garambawul na gwamnati da nufin sake tsara manyan shugabannin gwamnati.

Shugaba Kiir ya sanar da sauke Ohisa tare da maye gurbinsa da Addis Ababa Othow wanda a baya ya yi aiki a matsayin gwamnan babban bankin tsakanin watan Yuni da Nuwamba na bara.

Ba a bayar da wani dalili a hukumance na korarsa ba.

KARANTA KUMA: Gwamnan CBN, DG na WTO Ya Inganta Ciniki Tsakanin Afirka

Wannan sabon mataki ya zo ne a daidai lokacin da aka samu sauye-sauye a manyan mukamai na gwamnati a cikin ‘yan watannin nan, wanda masu sharhi kan siyasa suka ce yana nuna kokarin da shugaban kasa ke yi na karfafa iko a tsakanin rashin tabbas kan gadon siyasa.

An sake nada Ohisa, masanin tattalin arziki, a matsayin gwamnan babban bankin kasar a farkon wannan shekarar bayan ya yi wa’adi biyu daban-daban a matsayin.

Sudan ta Kudu na ci gaba da fama da kalubalen tattalin arziki masu tsanani, ciki har da raguwar kudaden shiga na mai, karancin kudi da ake fama da shi, hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudin kasar.

 

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button