Kwanciyar Hankali Ta Dawo Babban Birnin Nijar Bayan Rashin Nasarar Boren Sojoji
Sulaiman Ibrahim Muhammad

Rayuwa a Niamey ta koma kamar da kwanaki bayan da gwamnatin soja ta Nijar ta dakatar da bore da sojoji suka yi.
An yi mummunan fada a safiyar Asabar kafin a tsare sojoji da dama. An kashe wasu da dama yayin da suke kokarin kutsa kai cikin fadar shugaban kasa.
KARANTA KUMA: Sojojin Nijar Sun Yaki Masu Tawaye Kusa da Filin Jirgin Saman Babban Birnin
An ruwaito cewa sojojin ba su ji dadin gazawar gwamnati na dakile ayyukan ‘yan bindiga a kasar ba.
Wannan ne karo na uku da babban birnin ya ga ana fafatawa a wannan shekarar amma abubuwa biyu da suka gabata sun hada da masu jihadi da suka kai hari kan wani muhimmin sansanin soja a cikin filin jirgin.
“Da zarar an yi bore hakan na nufin abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata” cewar Hassane Assoumane mazaunin Niamey a ranar Lahadi.
“Wannan na nufin cewa watakila sojoji suna da abin da za su nema, kuma yanzu ya rage ga hukumomin da ke kan mulki su nemo mafita.”
Shugaban Nijar Janar Abdourahmane Tiani ya hau mulki a wani juyin mulki shekaru uku da suka gabata yana mai alƙawarin inganta tsaro.
Amma gwamnatinsa ta sha fama wajen dakatar da hare-haren da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da abin da ake kira daular Musulunci da kuma Al-Qaeda ke kai wa.
Tiani ya yanke alaƙa da tsohuwar ƙasar da ta yi wa mulkin mallaka ta Faransa kuma ya nemi goyon baya daga wasu abokan hulɗa ciki har da IranTurkiyya da Rasha.
An ruwaito cewa rundunar sojojin sa kai ta Afirka ta Rasha ta taimaka wajen dakile boren da aka yi ranar Asabar.
Africanews/Sulaiman Ibrahim Muhammad.



