Hadarin Jirgin Helikwafta Na Italiya A Bosnia Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Hudu Tare Da Jikkata Wasu 11

Ma’aikatar Tsaron Italiya ta sanar cewa, wani jirgin helikwafta na sojan Italiya wanda ke aiki a karkashin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Turai a Bosnia da Herzegovina ya yi hatsari a ranar Alhamis. Hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu 11.
Ma’aikatar ta bayyana cewa biyu daga cikin wadanda suka mutu sojojin Italiya ne yayin da sauran biyun kuma mambobi ne na rundunar sa-kai ta kungiyar Red Cross ta Italiya.
Ta kara da cewa dukkan mutane 11 da suka jikkata suna samun kulawar likitoci kuma babu wanda ke cikin halin da zai sanya rayuwarsa cikin hadari mai tsanani.
Jimillar mutane 15 ne ke cikin jirgin a lokacin da ya yi hatsarin.
Ministan Tsaron Italiya Guido Crosetto ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa inda ya bayyana lamarin a matsayin lokaci na tsananin bakin ciki.
Ya ce: “A wannan lokaci na tsananin bakin ciki tunanina yana tare da iyalan wadanda muka rasa da farko. Ina mika musu ta’aziyyata ta kashin kai, da kuma ta’aziyyar dukkan ma’aikatar Tsaro.”
KARANTA KUMA: Hatsarin Jirgin Masu Yawon Bude Ido a Peru Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 13 Kusa da Nazca Lines
Kamfanin dillancin labarai na Italiya ANSA ya rawaito cewa jirgin ya fadi ne a kauyen Gorice da ke gundumar Brcko.
Hotunan da kafofin yada labarai na yankin suka wallafa sun nuna jirgin sojan wanda ake amfani da shi wajen jigilar kaya ko mutane a juye a kasa kuma ya farfashe gunduwa-gunduwa.
Crosetto ya ce: “Babu kalmomin da za su iya rage radadin irin wannan babban rashi.”
Jirgin yana aiki ne a karkashin ‘Operation Althea’ wato tawagar Tarayyar Turai (EUFOR) da ke da alhakin sa ido kan aiwatar da Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta Dayton wadda ta kawo karshen yakin Bosnia.
Ma’aikatar Tsaron Italiya ta bayyana cewa an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin da kuma yanayin da ya faru a lokacin.



