
Kamfanin Deloitte Africa ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan gyare-gyaren da ake gudanarwa a fannin kudi da harkokin tattalin arziki a kasar, tare da karfafa masa gwiwar ci gaba da kulla kyakkyawar dangantaka mai karfafa zuba jari, horar da matasa, da samar da ayyukan yi.
Shugaban, wanda ya karbi tawagar Deloitte Africa karkashin jagorancin Babban Jami’in Gudanarwarta (CEO), Ruwayda Redfearn, a ranar Laraba da ta gabata a Fadar Shugaban Kasa, ya bayyana cewa gyare-gyaren sun taimaka wajen daidaita tattalin arziki a hankali cikin shekaru uku da suka gabata, tare da samun karbuwa da kuma alamun ci gaba mai kyau.
“Muna koyi da irin kwarewa da daukakar Deloitte wajen kawo sauyi daga tushe, domin gina makoma mai kyau ga al’ummarmu.
“Hakika, gyare-gyare suna da wahala. Ba abu ne mai sauki ko na gaggawa ba, amma idan aka aiwatar da su yadda ya kamata, suna samar da sakamako mai kyau, kuma shi ne abin da muke mayar da hankali a kai.
“Mun gode da irin hadin gwiwa da kulawar da kuke nunawa ga ayyukan da muke yi a nan, kamar yadda muka ji daga bakin Ministan Kudi game da gyare-gyaren da aka yi a fannin harkokin kudi, samar da kudaden shiga, da haraji, wadanda ke ciyar da kasar gaba.
“Gyare-gyaren da suka shafi kudaden shiga za su ci gaba da karfafa ci gaba. Kuma mene ne sakamakon gyare-gyaren? Hakika, akwai lokutan da ake fuskantar kalubale masu wuyar shawo kai—kamar shan magani mai daci—amma suna haifar da sakamako mai kyau. Dangane da tattalin arziki, Najeriya na samun gagarumin ci gaba daga tushe,” in ji Shugaban.
Har ila yau, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gyare-gyaren sun karfafa tattalin arziki, sun inganta bangarorin kudi da samar da kudaden shiga, sun sake tsara cibiyoyin hada-hadar kudi, tare da shirya kasar don samun karbuwa da kuma damar yin takara a matakin duniya.
KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu ya yi kira da a sake fasalin tsarin harkokin kudi na duniya
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa, Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, Shugaban ya bukaci kamfanin Deloitte Africa da su kara karfafa tasirinsu a fannin tattalin arzikin Najeriya ta hanyar horarwa da daukar matasan kasar masu kwazo aiki.
“Iyalan Deloitte; kun tuna min da lokutan farko na aikina a fannin lissafin kudi da kuma inda na fara koyon aikin a birnin Chicago. Deloitte tana da shirin horarwa mai kyau, kuma na yi imani za ku ci gaba da nuna hakan,” in ji shi.
Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da harkokin tattalin arziki, Mista Wale Edun, wanda ya yi magana kan batun sake fasalin da tasirinsa, ya bukaci shugabancin kamfanin na lissafin kudi da kasuwanci da su mayar da hankali wajen bunkasa kwarewar matasan Najeriya.
Shugabar kamfanin Deloitte Africa, Ruwayda Redfearn, ta bayyana cewa kamfanin na duniya yana mayar da hankali sosai kan sauye-sauye a fannin fasahar zamani da harkokin kasuwanci, inda yake da ma’aikata sama da 500,000 a duniya baki daya da ke gudanar da ayyuka daban-daban a wurare daban-daban, ciki har da sama da ma’aikata 6,000 a Afirka.
Ta ce kudaden shigar kamfanin na lissafin kudi sun kai dala biliyan 74 a shekarar 2025.
Babban Jami’in Gudanarwa na Deloitte Africa, Yomi Olugbenro, ya tabbatar wa Shugaban kasa cewa kamfanin zai bayar da goyon baya ga wadannan sauye-sauye, inda ya ce Deloitte za ta yi amfani da kwarewarta da gogewarta ta duniya wajen taimakawa da zurfafa wadannan sauye-sauye da kuma tabbatar da cewa fa’idodinsu sun isa ga talakawan Najeriya.
Aisha.Yahaya, Lagos



