Najeriya

COAS Ya Yaba Wa Nasarawa Bisa Goyon Bayan Fadada Sassan Sojoji

Babban Hafsan Sojin Kasa Laftanar Janar Waidi Shaibu ya yaba wa Gwamnatin Jihar Nasarawa bisa goyon bayan da take bai wa sabbin rukunai da sassan Sojin Najeriya inda ya bayyana wannan hadin gwiwa a matsayin mai matukar muhimmanci ga shirye-shiryen gudanar da ayyukan soja da kuma tsaron kasa.

Shaibu ya yi wannan yabo ne a ranar Juma’a 9 ga Oktoba 2026 yayin ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Abdullahi Sule a Gidan Gwamnati da ke Lafia.

Ziyarar ta kasance wani bangare na rangadin tantance ayyukan soja da kuma shirye-shiryen bikin kammala horon cikakken bataliyar Sojoji na Musamman (Special Forces) a Makarantar Sojojin Musamman ta Sojin Najeriya da ke Doma.

KARANTA KUMA: Babban Hafsan Soja Ya Yaba Da Kokarin Sojoji A Ayyukan Tsaro

A cikin wata sanarwa Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soji Kanar Appolonia Anele ya bayyana cewa Babban Hafsan Sojin ya nuna godiyarsa ga gwamna da kuma al’ummar Jihar Nasarawa bisa samar da yanayi mai kyau da kuma muhimman kayan aiki domin kafa da gudanar da sabbin rukunin sojin yadda ya kamata.

Shaibu ya bayyana cewa ziyarar ta kuma ba da damar tantance shirye-shiryen gudanar da ayyuka da tsare-tsaren gudanarwa na sabbin rundunoni da sassan da aka kafa.

Ya yi nuni da cewa fadada rundunar sojin Najeriya daga rukunai takwas zuwa 12 na bukatar karfafa karfin gudanar da ayyuka inganta tsarin tura sojoji da kuma karfafa hadin gwiwa tare da gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki a fannin tsaro.

Kasancewar jihar Nasarawa na karbar bakuncin rukunai da sassan rundunar soji da dama ciki har da Makarantar Sojojin Musamman ta Rundunar Sojin Najeriya ana sa ran karuwar kasancewar sojojin zai inganta tsaro ya kara inganci wajen tunkarar sabbin barazanar tsaro tare da karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa ta Tsakiya.

A jawabinsa na mayar da martani Gwamna Sule ya nuna godiyarsa ga Babban Hafsan Sojin Kasa bisa kafa wadannan rukunai na soji a jihar inda ya bayyana kasancewarsu a matsayin mataki mai muhimmanci wajen inganta tsaro da kuma samar da yanayi mai kyau ga harkokin zamantakewa da tattalin arziki.

Gwamnan ya ba wa Rundunar Sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro tabbacin ci gaba da samun goyon baya da hadin gwiwa daga gwamnatinsa domin dorewar zaman lafiya da kuma bai wa wadannan hukumomi damar gudanar da ayyukansu na tsarin mulki yadda ya kamata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button