Afirka

Kamaru Ta Sanya Ranar Zaɓen ‘Yan Majalisa Da Na Kananan Hukumomi A Watan Fabrairu

Shugaban Kamaru Paul Biya ya sanar da cewa za a gudanar da zaɓen ‘yan majalisu da na ƙananan hukumomi a ranar 7 ga Fabrairu, 2027.

Biya mai shekaru 93 ya sanar da hakan ne a cikin wata doka da aka karanta a rediyon jama’a a ranar Litinin fa ta gabata a tsakiyar rikicin siyasa a ƙasar kimanin shekara guda bayan zaɓen da ya tabbatar masa da wani wa’adi na biyu a kan mulki.

Biya wanda ya mulki Kamaru tun 1982 shi ne shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya.

Sake zaɓensa a watan Oktoba na 2025 ya haifar da zanga-zanga mai yawa wanda hukumomi suka gamu da shi da matakan tsaro.

KARANTA KUMA: Shugaban Kamaru Ya Koma Gida Bayan Kwanaki 73 a Ƙasashen Waje

Hukumomin sun dage zaɓen ‘yan majalisu da na ƙananan hukumomi na Kamaru sau biyu inda suka tsawaita wa’adin ‘yan majalisu har zuwa 20 ga Disamba 2026 da kuma na kansilolin ƙananan hukumomi har zuwa 28 ga Fabrairu 2027.

Ƙasar kuma tana jiran sake fasalin gwamnati da aka sanar kusan shekara guda da ta gabata da kuma naɗa mataimakin shugaban ƙasa.

Wani gyara a kundin tsarin mulki a watan Afrilun 2026 ya sake dawo da mukamin mataimakin shugaban kasa wanda ake sa ran zai gaji Biya idan ya mutu.

Tambayoyi game da lafiyar Shugaban kasa sun ci gaba da jan hankali inda yawan zama a kasashen waje ke kara ruruta muhawara kan ikonsa na mulki.

Duk da haka an haramta tattaunawa kan lafiyar Biya a kafafen yada labarai tun daga shekarar 2024 lokacin da jita-jita ke yawo game da mutuwarsa.

 

 

Al Jazeera/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button