AfirkaDuniya

Koriya Ta Kudu Da Masar Sun Ƙaddamar Da Ƙarfafa Alaƙa Tsakaninsu

Shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae Myung ya ce Koriya ta Kudu da Masar sun inganta dangantakarsu zuwa kawance mai mahimmanci.

Lee ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Seoul yayin da yake gabatar da jawabin bude taron da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi.

Shugabannin biyu sun kuma shaida sanya hannu kan wasu Takardun Fahimta (MoUs) da suka shafi gina jiragen ruwa makamashi mai tsafta kayayyakin more rayuwa na wutar lantarki da fasaha.

Lee ya ce Koriya ta Kudu na fatan kasashen biyu za su fara tattaunawa don aiwatar da Yarjejeniyar Hadin Gwiwa ta Tattalin Arziki (CEPA) don kara karfafa ciniki da zuba jari.

KARANTA KUMA:http://Koriya ta Kudu da Japan za su karfafa hadin gwiwar tsaro

Shugaban Koriya ta Kudu ya kuma ce kasashen biyu za su fadada hadin gwiwar tsaro yana mai bayyana hadin gwiwar samar da hoitzers masu sarrafa kansu na K9 a matsayin nasara.

Ya kara da cewa ya bayyana ka’idar Koriya ta Kudu ta zama tare cikin lumana a yankin Koriya ga Shugaba Sisi.

Ziyarar shugaban Masar ta biyo bayan taron koli tsakanin shugabannin biyu a birnin Alkahira a shekarar 2025.

Ana sa ran taron na baya-bayan nan zai kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin Koriya ta Kudu da Masar a fannin tattalin arziki makamashi tsaro da fasaha.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button