Najeriya

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 20 Da Aka Sace Wadanda Ke Shirin Shiga Shirin NYSC

Jami’an tsaro sun ceto mutane 20 da ke shirin shiga shirin bautar kasa (NYSC) wadanda aka sace a Jihar Imo a ranar 1 ga Oktoba 2026.

An ceto wadannan mutane ne da misalin karfe 4:28 na yamma a ranar Laraba 7 ga Oktoba a kauyen Amakohia Ubi da ke Jihar Imo bayan ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da ceto da ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro suka yi.

A cewar sanarwar da Kakakin rundunar ‘yan sanda CSP Ani Iniedu ya fitar an samu nasarar ceton ne sakamakon hadin gwiwa da hukumomin tsaron da suka shiga aikin suka yi.

Tuni aka kai wadanda aka ceto din domin a duba lafiyarsu tare da ba su kulawar likita da ta dace a matsayin wani bangare na matakan da ake bi bayan an ceto mutane.

A daya bangaren kuma hukumomin tsaro sun kara kaimi wajen gano tare da cafke wadanda ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da mutanen.

KARANTA KUMA:http://Kakakin Majalisa Abbas ya yaba da nasarar ceto mutanen da aka sace a Oyo

‘Yan sandan sun bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan har sai an gurfanar da wadanda ke da alhakin aikata laifin a gaban kuliya.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gode wa jama’a bisa hadin kai da goyon bayan da suka bayar tare da sake jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyi da kuma daukar matakan gaggawa wajen tunkarar duk wani barazana ga tsaron jama’a.

‘Yan sandan sun ce za su ci gaba da bayar da karin bayani idan bukatar hakan ta taso.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button