Fitattun LabaraiNajeriya

Shugaba Tinubu Ya Nuna Bakin Cikin Shi Na Rasuwar Sakatare-Janar Na Majalisar Shari’a

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana bakin cikinsa game da rasuwar Sakatare-Janar na Babban Majalisar Shari’a ta Najeriya (SCSN) Malam Nafiu Baba-Ahmed.

Shugaba Tinubu ya bayyana marigayi Baba-Ahmed a matsayin shugaba mai tasiri wanda ya jagoranci harkokin Babban Majalisar Shari’a ta Najeriya cikin hikima da hangen nesa da kuma jajircewa wajen tabbatar da hadin kai da adalci da zaman lafiya tsakanin al’umma.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu Shugaban ya jinjina wa “rawar da Malam Baba-Ahmed ya taka wajen tabbatar da ci gaba da jin muryar Majalisar kan batutuwan kasa da karfafa fahimtar juna da kuma inganta dabi’un gyaran tarbiyya da adalci a cikin al’umma.”

KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Sakatare-Janar na NLC

Shugaban ya tuna dadaddiyar alakar da ke tsakaninsa da marigayi Baba-Ahmed musamman a lokacin shirye-shiryen zaben 2011 da kuma shekarun da suka biyo baya tare da tunawa da shawarwari da goyon bayan da marigayin ya bayar yayin yakin neman zabensa na shugaban kasa a shekarar 2023.

Ya mika sakon ta’aziyya ga Shugaban Babban Majalisar Shari’a ta Najeriya da mambobinta da iyalan Baba-Ahmed da gwamnati da al’ummar Jihar Kaduna da kuma daukacin al’ummar Musulmin Najeriya bisa wannan babban rashi.

Shugaban ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta kurakuransa Ya sanya shi a cikin Aljannar Firdausi tare da bai wa iyalansa da al’ummar Musulmi hakuri da juriya na jure wannan rashi.

Malam Baba-Ahmed wanda ya kasance kwararren mai gudanarwa kuma shugaban addini ya rasu ne da safiyar ranar Talata bayan ya yi rayuwa mai cike da ayyukan alheri ga addinin Musulunci da kuma kasa baki daya.

 

 

Ladan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button