Kenya Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Ebola Ta Farko Da Aka Shigo Da Ita Daga Kwango

Ma’aikatar Lafiya ta Kenya ta tabbatar da bullar cutar Ebola ta farko a kasar da ta fito daga waje bayan da wani dan kasar Kenya ya iso daga Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ta hanyar Yuganda.
Ministan Lafiya Aden Duale ya bayyana cewa majiyyacin wanda ya iso Kenya ranar Asabar ya fara nuna alamun zazzabin da ke haifar da zubar jini (hemorrhagic fever) kuma aka kwantar da shi a Asibitin Nairobi inda gwaji ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar Ebola.
Duale ya ce: “Majiyyacin ya rasu a makare ranar Litinin yayin da ake ci gaba da ba shi kulawar likita.”
Ya kara da cewa: “Jami’an lafiya sun sanya kasar cikin shirin ko-ta-kwana kuma suna sa ido kan yiwuwar samun karin wadanda suka kamu da cutar.”
KARANTA KUMA: Yawan masu dauke da Ebola a DRC ya haura 8,000 yayin da adadin wadanda suka mutu ya kusa kai 4,000
A cewar Ministan an gano mutane 28 da suka yi mu’amala da majiyyacin ciki har da ‘yan uwansa da ma’aikatan lafiyar da suka kula da shi.
Ya kara da cewa “ana kuma ci gaba da neman wasu fasinjoji 23 da suka yi tafiya a jirgin saman da ya taso daga Yuganda tare da shi.”
Daraktan Ma’aikatar Patrick Amoth ya ce za a killace wadannan mutane da suka yi mu’amala da majiyyacin na tsawon kwanaki 21 kuma za a sake su bayan gwaji ya nuna ba su dauke da kwayar cutar.
Amoth ya ce za a binne mamacin cikin sa’o’i 24 bisa bin ka’idojin lafiyar jama’a da tsaro da aka ba da shawarar bi.
Kenya ce kasa ta hudu da ta bayar da rahoton bullar cutar Ebola a wannan annoba ta yanzu wadda aka sanar da bullarta a gabashin Congo a tsakiyar watan Mayu.
Yuganda ta sami mutane 20 da suka kamu da cutar yayin da Faransa ta bayar da rahoton mutum ɗaya. Kafin sabuwar cutar da ta bulla a Kenya babu wani mai dauke da cutar Ebola a wajen Kwango tun lokacin da Yuganda ta ayyana barkewar cutar a ƙarshen watan Agusta.
Barkewar cutar ta samo asali ne daga ƙwayar cutar Bundibugyo mai saurin yaduwa wadda a halin yanzu babu wani allurar rigakafi ko magani da aka amince da ita.
Ana gudanar da gwaje-gwajen rigakafi da magani a lardin Ituri na Kwango cibiyar barkewar cutar.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa barkewar cutar na iya zama mafi muni idan ƙoƙarin gano da kuma shawo kan cutar ya gaza ci gaba da yaɗuwa.
AP/ Ladan Nasidi



