Nishadi.

Yan Sandan Kano Sun Karfafa Tsaro A Wuraren Da Ake Gudanar Da Bukukuwan Hawan Dawaki

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ta sanya dokar sanar da ita sa’o’i 72 kafin gudanar da duk wani bikin Durbar ko hawan dawaki da sauran dabbobi a wuraren jama’a a fadin jihar.

Wannan mataki na da nufin bai wa hukumomin tsaro damar tantance yanayin tsaro da kuma tura jami’ai yadda ya kamata kafin gudanar da irin wadannan taruka.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar CP Ibrahim Bakori ne ya sanar da wannan sabuwar doka yayin wani taron manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda ta Bompai Kano.

KARANTA KUMA: http://Gwamnan Kano Zai Ci Gaba da Gyare-gyare da Kammala Ayyuka

Ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne biyo bayan kudurin da aka cimma a taron hadin gwiwa na hukumomin tsaron jihar  sakamakon damuwa game da rahotannin da ke nuna ana karya dokar da aka sanya a baya ta hana gudanar da bukukuwan Durbar da hawan dawaki.

CP Bakori ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano ce ta sanya wannan doka ta hana gudanar da bukukuwan bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin tsaro a matsayin wani bangare na matakan kare lafiyar jama’a da kuma tabbatar da zaman lafiya da oda.

Ya ce har yanzu akwai barazanar tsaro da ta sa aka sanya dokar inda ya jaddada cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da daukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

A karkashin wannan sabon tsari na hadin gwiwar tsaro duk wani mutum cibiya ko kungiya da ke son gudanar da bikin Durbar ko hawan dawaki/dabbobi a wurin jama’a dole ne ta mika sanarwa a rubuce ga Rundunar ‘Yan Sanda ta hanyar Ofishin Kwamishinan ‘Yan Sanda akalla sa’o’i 72 kafin lokacin da aka tsara gudanar da taron.

Kwamishinan ya ce wannan sanarwa za ta bai wa rundunar damar tantance yanayin tsaron taron da kuma shirya matakan da suka dace domin kare mahalarta taron mazauna yankin da sauran jama’a.

Ya yi kira ga mazauna jihar da kungiyoyi da su bi wannan doka tare da ba hukumomin tsaro hadin kai inda ya yi gargadi game da duk wani aiki da zai iya kawo barazana ga tsaron jama’a.

CP Bakori ya tabbatar wa mazauna jihar cewa hukumomin tsaro a Kano za su ci gaba da yin aiki tare wajen tabbatar da aiwatar da dokoki da kuma kula da zaman lafiya da oda a fadin jihar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button